Da ace Jonathan ya biya Jihar Osun kudin ta da ba haka ba - Aregbesola

Da ace Jonathan ya biya Jihar Osun kudin ta da ba haka ba - Aregbesola

- Gwamna Aregbesola yace fiye da Tiriliyan 8 su ka yi dabo lokacin Jonathan

- Gwamnan na Osun ya fadi abin da ya sa ake bin sa bashin albashin Ma’aikata

- Aregbesola yace sai dai wanda zai gaje shi yanzu zai samu Gwamnati a sama

Mun samu labari cewa a makon nan ne Gwamnan Jihar Osun watau Rauf Ogbeni Aregbesola ya fito bayyana irin makudan kudin da su ka bace a lokacin Goodluck Jonathan yana mulkin kasar nan.

Da ace Jonathan ya biya Jihar Osun kudin ta da ba haka ba - Aregbesola

Gwamnan Jihar Osun Aregbesola ya cika shekara 61 a Duniya.

Mai Girma Gwamna Rauf Aregbesola yace a lokacin Gwamnatin Jonathan Tiriliyoyin kudin Kasar sun shige hannun wasu tsirarrun Jami’an Gwamnati ne. Gwamnan ya bayyana wannan ne lokacin bikin taya sa murnar cika shekaru 61 da haihuwa.

Gwamnan na Jihar Osun yace akalla Naira Tiliyan 8.1 da ya kamata su dawo hannun Gwamnatin Tarayya a san inda su ka shige ba a lokacin Jonathan. Gwamnan na APC yace da ace wadannan kudi sun shigo hannun Gwamnati da ba haka ba.

KU KARANTA: Tun da na hau mulki ban taba karbar albashi ba – Aregbesola

Rauf Aregbesola yake cewa kason Jihar sa daga cikin wadannan Tiriliyoyi ya kai Naira Biliyan 75, kuma da ace Gwamnatin Jihar Osun ta samu wannan kudi da an biya Ma’aikata duk albashin su har ta kai a biya bashin da ake bin Jihar.

Daily Trust ta rahoto cewa Gwamnatin Jihar Osun za ta kammala biyan bashin da ta ci nan da shekara mai zuwa. Gwamna Aregbesola da wa’adin sa ya kusa zuwa karshe yace wanda dai zai gaje sa zai ci banza ne kurum a Gwamnati.

Dama kun ji labari cewa tsohon Shugaban Kasar Dr. Goodluck Jonathan ya karyata zargin sata inda yace sai da ya kammala ayyuka sama da 1000 a lokacin da yake rike da Kasar nan tsakanin 2010 zuwa 2015.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel