Rikicin APC: Abin da Oshiomhole su ka tattauna da ‘Yan Majalisa

Rikicin APC: Abin da Oshiomhole su ka tattauna da ‘Yan Majalisa

- Adams Oshiomhole na neman kujerar Shugaban Jam’iyyar APC na kasa

- Tsohon Gwamna Oshiomhole ya ji ta-bakin ‘Yan Majalisar APC kwanaki

- Oshimhole yace idan ya zama shugaba to APC za ta ba kowa hakkin sa

Tsohon Gwamnan Jihar Edo Adams Oshiomhole wanda yanzu haka yake neman kujerar Shugaban Jam’iyyar APC na kasa ya gana da ‘Yan Majalisar Jam’iyyar APC mai mulki a makon da ya gabata.

Rikicin APC: Abin da Oshiomhole su ka tattauna da ‘Yan Majalisa

Adams Oshiomhole yace idan ya gaji Oyegun zai yi maganin sabanin APC

Kwamared Adams Oshiomhole ya kai wa Sanatocin Kasar ziyara ne domin su mara masa baya ya samu kujerar Shugaban APC. Lokacin da aka zanta, Sanatocin Jam’iyyar mai mulki sun kai kukan su gaban tsohon Gwamnan na Edo.

KU KARANTA: Atiku ya bude wani katafaren ofishin kamfe domin 2019

Kamar yadda mu ka samu labari daga Jaridar Vanguard, Saraki da sauran ‘Yan Majalisar Dattawa sun bayyanawa Oshiomhole yadda abubuwa su ka tabarbare a Jam’iyyar. Ana sa rai ‘Dan takarar zai dinke barakar da ke cikin APC.

Kuma bisa dukkan alamu dai ‘Yan Majalisar APC ba su da niyyar sauya sheka bayan da su ka gamsu cewa Oshiomhole zai yi maganin duk rikicin da ya shigo Jam’iyyar. Oshimhole yace ba zai danne kowa ba idan ya zama shugaba.

Haka kuma tsohon Gwamnan ya nuna cewa idan ya samu wannan kujera to zai tafi da kowa a Jam’iyyar domin kuwa babu wanda ya tattara sanin komai. Oshiomhole ya kuma a siyasa kowa bai samun yadda yake so sai dai a nemi maslaha.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel