Rikicin Jam'iyyar APC: Za'ayi zaman karshe tsakanin sabuwar jam'iyyar nPDP, shugaba Buhari da Osinbajo a yau

Rikicin Jam'iyyar APC: Za'ayi zaman karshe tsakanin sabuwar jam'iyyar nPDP, shugaba Buhari da Osinbajo a yau

- A cigaba da tattaunawa akan matsalolin da jam'iyyar APC mai mulki ke fuskanta, wanda sabuwar jam'iyyar nPDP ke kawo wa, sabuwar jam'iyyar ta shirya wani sabon taro tsakanin ta da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, wanda za'ayi zaman a yau dinnan

- Ana saran masu halartar taron zasu hadu da Shugaban kasa Muhammadu Buhari don sanar dashi sakamakon taron

Rikicin Jam'iyyar APC: Za'ayi zaman karshe tsakanin sabuwar jam'iyyar nPDP, shugaba Buhari da Osinbajo a yau

Rikicin Jam'iyyar APC: Za'ayi zaman karshe tsakanin sabuwar jam'iyyar nPDP, shugaba Buhari da Osinbajo a yau

A cigaba da tattaunawa akan matsalolin da jam'iyyar APC mai mulki ke fuskanta, wanda sabuwar jam'iyyar nPDP ke kawo wa, sabuwar jam'iyyar ta shirya wani sabon taro tsakanin ta da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, wanda za'ayi zaman a yau dinnan. Ana saran masu halartar taron zasu hadu da Shugaban kasa Muhammadu Buhari don sanar dashi sakamakon taron.

DUBA WANNAN: Fadar shugaban kasa ta bankado yadda Obasanjo ya tsige wasu gwamnoni ba bisa ka’ida ba

Sabuwar jam'iyyar ta nPDP wacce ta samu jagorancin tsohon shugaban jam'iyyar PDP mai rikon kwarya, Alhaji Abubakar Kawu Baraje, sun hadu da jiga-jigan jam'iyyar a satin daya gabata, don tattaunawa akan matsalolin da suke fuskanta.

Baraje ya tabbatar da taron nasu ga manema labarai a Ilorin babban birnin Kwara, inda yace zasu hadu da shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma mataimakin sa Yemi Osinbajo a ranar Litinin dinnan.

Baraje yayi kyakkyawan fata na cewa yana fatan taron nasu na yau tare da shugabannin zai kawo karshen matsalolin da suke fuskanta a jam'iyyar.

Yace taron nasu na yau shine zai bayyana musu matakin da sabuwar jam'iyyar ta su ta nPDP zata dauka.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel