Shuwagabannin Najeriya tambararrun barayi ne – Shehin Malami Farfesa Ishaq

Shuwagabannin Najeriya tambararrun barayi ne – Shehin Malami Farfesa Ishaq

Shugaban hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandari, JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede ya bayyana cewa mutanen dake shugabantar Najeriya kwararru ne kuma tambararru a harkar sata, masu digir digirgir a sata, inji rahoton jaridar Premium Times.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Ishaq ya bayyana haka ne yayin taron bikin zagayowar ranar haihuwar gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola a ranar Lahadi, 27 ga watan Mayu, a garin Osun, inda yace Ilimi ya tabarbare ne sakamakon tambararrun barayi da suka shugabanci Najeriya.

KU KARANTA: Cinnen EFCC: Cikin jiga jigan yayan jam’iyyar PDP ya duri ruwa

Ishaq yace bambancin kudaden shiga da hukumar JAMB ta tara a shekarun baya da wanda ta tara a karkashinsa ya tabbatar da cewar barayi ne suka shugabanci hukumar a baya, wadanda suka kaurin suna a fagen cin hanci da rashawa.

Shuwagabannin Najeriya tambararrun barayi ne – Shehin Malami Farfesa Ishaq

Shehin Malami Farfesa Ishaq

“Tambararrun barayi ne suka mamaye Najeriya, misali a sama da shekaru 40 da aka kafa JAMB, naira miliyan 52 kacal ta samar ma gwamnati a matsayin kudaden shiga, amma a shekarar 2017, an tara naira biliyan 9, a shekarar nan ma mun tara sama da naira biliyan 9.” Inji shi.

Hakazalika Farfesan ya bayyana ayyukan kungiyoyin matsafa da karuwanci a matsayin matsalolin da suka addabo makarantun gaba da sakandari, inda yace:

“Baka bukatar jefa bom a kasa kafin ta lalace, idan ka tabarbara ilimi a kasar ma ya isa ya yi rugu rugu da kasar. Don haka da kyakkyawan ilimi ne kadai za a iya samar da nagartattun mutane a kasa, Ingantaccen ilimi zai kawar da talauci a tsakanin yan kasa." Inji shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel