Ma’aikatan jirgin sama sun sacewa wani fasinja dalar Amurka miliyan $1.630m

Ma’aikatan jirgin sama sun sacewa wani fasinja dalar Amurka miliyan $1.630m

- Gwamnatin tarayya ta daukaka hukuncin wata kotu na sakin wasu ma’aikatan kamfanin safarar jiragen sama na Emirates

- Gwamnatin tarayya na son kotun daukaka kara ta jingine hukuncin kotun farko tare da bukatar kotun ta hukunta ma’aikatan 10 a kan bacewar kudin fasinja, $1,630,000

- A ranar 10 ga watan Afrilu ne mai shari’a Idris ya wanke dukkan wadanda aka zargin saboda rashin gamsashshiyar shaidar cewar sun saci kudin

Gwamnatin tarayya ta daukaka hukuncin wata kotu na sakin wasu ma’aikatan kamfanin safarar jiragen sama na Emirates bisa zargin su da hannu cikin batan kudin wani fasinja dake cikin bahunhuna hudu.

Gwamnatin tarayya na son kotun daukaka kara ta jingine hukuncin kotun farko da mai shari’a Mohammed idris ya yi tare da bukatar kotun ta hukunta ma’aikatan 10 a kan bacewar kudin, $1,630,000.

Ma’aikatan jirgin sama sun sacewa wani fasinja dalar Amurka miliyan $1.630m

Gudumar kotu

Gwamnatin tarayya ta gurfanar da mutanen 10 tare da kamfanin Emirate da wasu kamfanoni bisa hada baki wajen sace kudin fasinjan jirgin kuma dan kasuwa, Prince Chu Ikem Orji.

DUBA WANNAN: An gano gawar qwasu tagwaye a cikin firinjin gidan su bayan an bayyana bacewar su

Ana zargin su ne da sace buhunhunan kudin a filin tashi da saukan jiragen sama na Murtala Mohammed dake Legas ranar 19 ga watan Disamba na shekarar 2017. Kudin na cikin buhunhunan da aka yiwa lamba EK 428682, EK 428583, EK 650162, da EK 650161 da za a kaiwa dan kasuwar kasar China.

A ranar 10 ga watan Afrilu ne mai shari’a Idris ya wanke dukkan wadanda aka zargin saboda rashin gamsashshiyar shaidar cewar sun saci kudin.

Rashin gamsuwa da wannan hukunci ne ya saka gwamnatin tarayya garzayawa ya zuwa kotun daukaka kara dake jihar Legas.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel