Fadar shugaban kasa ta bankado yadda Obasanjo ya tsige wasu gwamnoni ba bisa ka’ida ba

Fadar shugaban kasa ta bankado yadda Obasanjo ya tsige wasu gwamnoni ba bisa ka’ida ba

Fadar shugaban kasa tab akin mai taimakawa shugaba Buhari a bangaren yada labarai, Mallam Garba Shehu, ta kara sukar shugaba Obasanjo a yau, Lahadi.

Mallam Shehu ya bayyana yadda tsohon shugaban kasa Obasanjo ya tsige wasu gwamnoni 5, ba bisa ka’ida ba, daga kujerun su lokacin yana mulki.

Da yake bayar da misalan irin gwamnoni ha hanyoyin da Obasanjo ya bi domin tsige su, Mallam Shehu, ya ce, ”’yan majalisa 5 sun tsige tsohon gwamnan jihar Filato, Joshua Dariye, da misalign karfe 6:00 na safe; kamar yadda ya saka ‘yan majalisa 18 daga jihar Oyo suka tsige tsohon gwamna, Rasheed Ladoja.

Fadar shugaban kasa ta bankado yadda Obasanjo ya tsige wasu gwamnoni ba bisa ka’ida ba

Mallam Garba Shehu

“A jihar Anambra ya yi kokarin tsige tshon gwamnan su, Peter Obi, amma hakan bata yiwu bayan ya gaza samun rinjayen ‘yan majalisar jihar. Laifin Obi shine yaki yin aringizon kudin kasafin jihar sa tare da kin komawa jam’iyyar PDP.”

DUBA WANNAN: Buhari zai mayar da hankali a kan wasu matsaloli biyu da suka addabi Najeriya

“A jihar Ekiti haka ya tsige gwamna Ayo Fayose a zangon san a farko bayan ya zarge shi da laifin cin hanci da kisan kai amma maimakon a bawa mataimakin sa rikon jihar kamar yadda doka ta tanada sai ya dauko soja, Birgediya Janar Adetunji Olurin (mai ritaya), ya nada a matsayin gwamnan soji na wucin gadi,” a cewar Mallam Shehu.

Mallam Shehu yak are da cewa duk irin wannan taka doka yanzu shugaba Buhari bay a aikata irin su saboda yana mutunta doka da kundin tsarin mulkin Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel