Saboda kwadayin mulki wasu su ka lullube Shugaban Kasa Buhari Inji Sanatan APC

Saboda kwadayin mulki wasu su ka lullube Shugaban Kasa Buhari Inji Sanatan APC

- Sanatan Kaduna Shehu Sani ya soki na kusa da Shugaban Kasa Buhari

- Shehu Sani ya nuna cewa kwadayin mulki ya sa wasu ke tare da Shugaban

- ‘Dan Majalisar na APC yace da zarar Shugaban Kasar ya bar mulki za su tsere

Sanata Shehu Sani wanda ya saba magana kan abubuwan da su ka shafi kasar nan yayi kaca-kaca da wadanda su ka zagaye Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ganin ya samu kujerar mulki.

Saboda kwadayin mulki wasu su ka lullube Shugaban Kasa Buhari Inji Sanatan APC

Sani ya fadawa Buhari ba a san ma ci tuwo ba sai miya ta kare

Kwamared Shehu Sani wanda ke wakiltar Kaduna ta tsakiya a Majalisar Dattawa karkashin APC yace wadanda ke bin Shugaba Muhammadu Buhari a gindi a yanzu su na yin haka ne domin yana rike da kujerar Shugaban Kasa.

KU KARANTA: Bi-ta-da-kulli Buhari ya ke yi - Sanata Baba-Ahmed

Sanatan yace da zarar Shugaba Buhari ya bar kujerar shugaban Kasa wadanda su ka zagaye kan su a Fadar Shugaban Kasar za su zame jikin su su bar shi. Sanata Sani yace a lokacin da Shugaba Buhari bai mulki ba su san da shi ba.

Shehu Sani yace dama da zarar an ce mutum ya samu mulki akwai wasu mutanen da su zagaye sa saboda kwadayi. Sanatan ya kuma dai yi kira a kawo karshen yajin aiki Malaman asibiti da ya ki ci ya kuma ki cinyewa a Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel