Wasu ‘Yan Majalisar Najeriya ba aikin da su ke yi sai lamuke albashi

Wasu ‘Yan Majalisar Najeriya ba aikin da su ke yi sai lamuke albashi

- Da dama dai daga cikin ‘Yan Majalisar Najeriya ba su wani aikin kirki

- Kaso mafi tsoka na ‘Yan Majalisar sun gagara gabatar da kudiri ko daya

- Hukumar CISLAC tace ‘Yan Majalisar ba su san aikin da aka tura su ba

A bara kusan war-haka ‘Yan Majalisar Arewa akalla 102 ba su gabatar da wani kudiri ba bayan shekaru a Majalisar. Daily Trust a wani bincike tace kashi kusan 65 cikin 100 na ‘Yan Majalisar da ke wakiltar Jihohin Arewa ci-ma-zaune ne.

Wasu ‘Yan Majalisar Najeriya ba aikin da su ke yi sai lamuke albashi

‘Yan Majalisar Najeriya da dama ba su aikin komai

‘Yan Majalisar da ke Arewa-maso-Gabashin Kasar akalla 25 cikin 48 da ake da su dai ba su gabatar da kudirin komai ba. Haka kuma guda 16 cikin 49 na ‘Yan Majalisar Arewa maso Arewacin Najeriyar dumama kujeru kurum su ke yi.

KU KARANTA: Sanatoci da ‘Yan Majalisu da wasu tsofaffin Gwamnonin na neman barin APC

Ragowar ‘Yan Majalisar Tarayyar da ke Yankin Shugaban Kasa Buhari na Arewa maso Yamma dai sama da 60 ba su da wani kudiri cikin shekara 3 da su kayi a Majalisar. ‘Yan Majalisa 91 ne su ke wakiltar Yankin na Arewacin Kasar.

Hukumar CISLAC ta bakin Darektan ta Auwal Musa Rafsanjani ta taba cewa ‘Yan Majalisar ba su san abin da su ke yi ba. Auwal Rafsanjani yace rashin sanin kan aiki ya sa ‘Yan Majalisar ba su iya tabuka komai sai son ran su da satar kudi.

Haka zalika dai ‘Yan Majalisar Kudancin Kasar da dama ba su wani aikin kirki a Majalisar. Kwanaki dai Shugaban Kasa Buhari yace wasu ‘Yan Majalisar ba su aikin fari ba su na baki a zaman su na tsawon shekaru.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel