Kaka-kara-kaka: Sanatoci 13 da da ake tuhuma da cin hanci da rashawa

Kaka-kara-kaka: Sanatoci 13 da da ake tuhuma da cin hanci da rashawa

- A cikin shekaru uku da Majalisar Dattijai ta 8 tayi za’a iya tunawa da ita ta fuskoki da dama walau na jinjina ko na Allah wadai.

- A watan Maris na 2018 Majalisar tai wani abu da za’a iya fasalta shi da yabon kai sakamakon cimma nasarar kafa tahirin zartar da kudurori 201 wanda kaf tun bayan dawowar Mulkin Dimukuradiyya ba a taba samun Majalisar da tayi abin a zo a gani kamarta ba, domin Majalisa ta 5 na da kudirai 28, yayinda Majalisa ta 6 ke da 25, ita kuma ta 7 ke da kudurai 65.

Kaka-kara-kaka: Sanatoci 13 da da ake tuhuma da cin hanci da rashawa

Kaka-kara-kaka: Sanatoci 13 da da ake tuhuma da cin hanci da rashawa

Sai dai kuma duk da irin waccan nasara zai yi wahala ‘yan kasa su manta da katankatanar da Majalisar ta kulla wajen zabar shuwagabanninta da kuma shigar burton da wasu tsagerun ‘yan daba su kayi inda ha su kayi awon gaba da sandar ikon Majalisar, sannan kuma da batun dakatar da Mambobinta da Majalisar take yi dalilin karamin laifin da bai taka kara ya karya ba.

Da kuma ruguntsumi gami da satoka-sakatsi da bangaren zartarwa da kuma jami’an Gwamnati.

To amma wani abu bayan wannan da ya kamata ku sani shi ne daga cikin Sanatoci 109 dake zauren Majalisar, alal-akalla 13 ana tuhumarsu da wata badakala ko almundahana ko kuma sama da fadi da dukiyar al’umma.

Yanzu haka batun da ake wasu na kotu suna fuskantar shari’a domin sanin makomarsu yayinda wasunsu kuma ke makare a hammatar EFCC ko ICPC. Sai dai kuma wani abin mamaki shi ne yadda kafataninsu suka kekasa kasa suka ki yarda da aikata laifi ko daya.

Bukola Saraki

Kaka-kara-kaka: Sanatoci 13 da da ake tuhuma da cin hanci da rashawa

Kaka-kara-kaka: Sanatoci 13 da da ake tuhuma da cin hanci da rashawa

Kafin watan Maris da aka dake shari’ar da ake yi masa shugaban Majalisar ya kasance yana yawan zuwa Kotun da’ar ma’aikata don cigaba da shari’ar zargin da ake yi masa na bayanan karya da ya bayar kan kadarorin da ya mallaka.

Ike Ekweremadu

Kaka-kara-kaka: Sanatoci 13 da da ake tuhuma da cin hanci da rashawa

Kaka-kara-kaka: Sanatoci 13 da da ake tuhuma da cin hanci da rashawa

Mataimakin shugaban Majalisar da shi kansa shugaban Majalisar da kuma karin wasu Mambobi biyu Akawun Majalisar Salisu Maikasuwa, da mataimakinsa Benedict Efeturi ana tuhumarsu ne bisa kwaskwarima da gabatar da wasu takardun bugi a wata kara da wasu daga cikin Sanatoci suka shigar a 2015.

Daga bisani Gwamnatin tarayya ta janye tuhumar da ake yiwa musu a 2016 amma kuma shi Mr Ekweremadu har yanzu tasa tana kasa tana dabo.

Dino Melaye

Kaka-kara-kaka: Sanatoci 13 da da ake tuhuma da cin hanci da rashawa

Kaka-kara-kaka: Sanatoci 13 da da ake tuhuma da cin hanci da rashawa

Yayi kaurin suna ba don komai sai don kasancewarsa mai yawan surutu kamar bakinsa yana yoyo. Yanzu haka Dino yana garkame a halarar tsaro ta jami’an ‘Yan sanda tun bayan da su kayi ram dda shi bisa zargin hada kai da kuma samar da Makamai ga wasu yan ta’adda da ak zarginsu da aikata muggan laifuka.

Haka zalika ana zarginsa da yunkurin kashe kansa yayinda jami’an tsaro ke hanyar kai shi jihar Kogi domin gurfanar da shi gaban alkali, wanda shi ma kuma babban laifi ne

Yanzu dai Kotu ta dakatar da shari’arsa sakamakon rashin lafiyarsa tun bayan dirgowa da yayi daga cikin motara ‘Yan sanda.

Peter Nwaboshi

Kaka-kara-kaka: Sanatoci 13 da da ake tuhuma da cin hanci da rashawa

Kaka-kara-kaka: Sanatoci 13 da da ake tuhuma da cin hanci da rashawa

Ba jimawa ne a watan Afrilu EFCC ta gurfanar da shi gaban kuliya bisa zargin shi da hadin baki tare da wasu kamfanoni biyu cikin wata badakalar N322m

Nan take mai shari’a Mohammed Idris na babbar kotun dake zamanta a Abuja ya umarci da ingiza keyarsa gidan kaso, kafin daga bisani ya samu beli bayan shafe kwanaki biyu a garkame.

Buruji Kashamu

Kaka-kara-kaka: Sanatoci 13 da da ake tuhuma da cin hanci da rashawa

Kaka-kara-kaka: Sanatoci 13 da da ake tuhuma da cin hanci da rashawa

A cikin watan Mayu na 2015, hukumar yaki da sha da fataucin mmiyagun kwayoyi (NDLEA) ta yiwa gidan Sanatan kawanya a wani yunkuri nay i masa kamun kazar kuku domin aikewa da shi can kasar Amurka don ya fuskanci tuhumar ta’ammali da muggan kwayoyi.

KU KARANTA: Bikin ranar dimokradiyya ba shi da amfani a Najeriya - PDP

Mr Kashamu ana neman sa ne domin amasa tuhumar ta’ammali da muggan kwayoyi a Amurka, lamarin da shi kuma ya karya ta. Yaki mika kansa, maimakon haka sai ya nufi Kotu ya kalubalanci yunkurin, Kotun kuma ta amsa rokonsa.

Ahmed Yarima

Kaka-kara-kaka: Sanatoci 13 da da ake tuhuma da cin hanci da rashawa

Kaka-kara-kaka: Sanatoci 13 da da ake tuhuma da cin hanci da rashawa

A shekarar 2016 ICPC ta gurfanar da shi bisa zarginsa da laifuka 19 da suke da alaka da cin hanci da rashawa.

Hukumar na zarginsa da laifin karkatar da akalar Naira biliyan daya (N1b) na wasu kudade da aka ware domin gyaran madatsar ruwa ta Gusau da kuma biyan diyya ga wadanda ambaliyan ruwan ya shafa.

Amma sai dai an sallame shi a watan Disambar 2017 sakamakon gaza gamsar da Kotu da masu kara (ICPC) su kayi.

David Mark

Kaka-kara-kaka: Sanatoci 13 da da ake tuhuma da cin hanci da rashawa

Kaka-kara-kaka: Sanatoci 13 da da ake tuhuma da cin hanci da rashawa

Shi ne tsohon shugaban Majalisar Dattijai kuma shi ma yana cikin wadanda EFCC ke tuhuma a watan Disambar 2017 da kuma watan Janairu na 2018 sakamakon wasu kudade da suka gifata wajen tafiyar da zaben 2015 har Naira biliyan N2b kasancewar shi yayi jagaban raba kudaden ga ragowar Sanatocin PDP.

Amma sai dai yaki amincewa da karbar kudaden da ake zargin na zaben 2015 wanda wannan ya kara sanya hukumomin yaki da cin hanci da rashawa kara fantsama domin neman wasu hujjojin.

Stella Oduah

Kaka-kara-kaka: Sanatoci 13 da da ake tuhuma da cin hanci da rashawa

Kaka-kara-kaka: Sanatoci 13 da da ake tuhuma da cin hanci da rashawa

Sanatar da ta fito daga jihar Anambra ita na daga cikin wadanda EFCC ke zargi da sama da fadi da wasu kudade masu nauyi.

A watan Fabarairu EFCC ta caje ta sosai har ma aka kwace mata Fasfo dinta. Kuma in za’a iya tunawa tana daga cikin wadanda Gwamnatin tarayya ta fitar da sunayensu a cikin jadawalin barayin kasa.

Yanzu haka ana tuhumarta bisa zargin bayar da wasu kwangiloli ba bisa ka’ida har na kusan Naira biliyan goma (N9.4b).

Danjuma Goje

Kaka-kara-kaka: Sanatoci 13 da da ake tuhuma da cin hanci da rashawa

Kaka-kara-kaka: Sanatoci 13 da da ake tuhuma da cin hanci da rashawa

Shi ma da wasu Mutane biyu yanzu haka na fuskantar tuhuma bayan da EFCC ta gurfanar da shi a gaban babbar Kotu dake zamanta a jihar Gombe bisa zargin sama da fadi da Naira bliyan N25b

Abdullahi Adamu

Kaka-kara-kaka: Sanatoci 13 da da ake tuhuma da cin hanci da rashawa

Kaka-kara-kaka: Sanatoci 13 da da ake tuhuma da cin hanci da rashawa

Sanata Abdullahi Adamu tsohon Gwamnan jihar Nassarwa EFCC ta kama shi a shekarar 2010 saboda almubazzaranci da kudin da ya kai Naira biliyan N15b tare da wasu karin Mutane 18 har yanzu ba’a kai ga kammala shari’ar ba.

Kuma a shekarar 2018 EFCC ta damke dansa Nuraini Adamu tare da wani Felix Onyeabo Ojiako sannan ta gurfanar da su gaban mai shari’a Farouq Lawal a jihar Kano bisa zarginsu da laifuka guda 4.

Abdulaziz Nyako

Kaka-kara-kaka: Sanatoci 13 da da ake tuhuma da cin hanci da rashawa

Kaka-kara-kaka: Sanatoci 13 da da ake tuhuma da cin hanci da rashawa

Sanatan Nyako mai wakiltar Adamawa ta tsakiya kuma da ga tsohon Gwamnan jihar Murtala Nyako yana fuskantar tuhuma daga EFCC kan kudin da ya kai Naira biliyan N29b. Ana dai tuhumarsa ne tare da shi da Mahaifinsa da kuma wasu Mutane biyu da laifuka har guda 37 da suka hada da hadin baki wajen kulla wata makarkashiya da babakere da kuma banzagalar da dokar aiki.

Joshua Dariye

Kaka-kara-kaka: Sanatoci 13 da da ake tuhuma da cin hanci da rashawa

Kaka-kara-kaka: Sanatoci 13 da da ake tuhuma da cin hanci da rashawa

EFCC na tuhumarsa ne da laifuka 6 wadanda suka hada da sama da fadi da Naira biliyan N15b sannan kuma ana sake tuhumarsa da wasu laifukan har guda 23 da suka danganci karkatar da akalar kudade masu nauyi har Naira biliyan N1.2b tun shekarar 2007.

Jonah Jang

Kaka-kara-kaka: Sanatoci 13 da da ake tuhuma da cin hanci da rashawa

Kaka-kara-kaka: Sanatoci 13 da da ake tuhuma da cin hanci da rashawa

Tsohon Gwamnan jihar Plateau yana fuskantar tuhuma daga hukumar EFCC tare da tsohon sakataren Gwamnatin jihar Yusuf Pam bisa zargin karkatar da akalar Naira biliyan N6.3b yayinda yake a rike da mukamin Gwamnan jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel