Sace sandan ikon majalisa: An canja DPO din ofishin ‘yan sanda dake cikin majalisa

Sace sandan ikon majalisa: An canja DPO din ofishin ‘yan sanda dake cikin majalisa

- An canjawa DPO din ofishin ‘yan sanda dake cikin ginin majalisar dattijai, CSP Abdul Sulu-Gambari, wurin aiki zuwa jihar Adamawa

- Sulu-Gambari ya shaidawa kwamitin bincike na majalisar dattijai cewar ya kama mutum shida dangane da batun sace sandar majalisar

- Saidai shelkwatar ‘yan sanda ta musanta cewar ta kama mutanen shidan ne saboda sace sandar majalisar

An canjawa DPO din ofishin ‘yan sanda dake cikin ginin majalisar dattijai, CSP Abdul Sulu-Gambari, wurin aiki zuwa jihar Adamawa. Tuni Sulu-Gambari ya kwashe kwamotsansa daga ofis tare da komawa Adamawa, kamar yadda jaridar Daily Trust a rawaito.

Sace sandan ikon majalisa: An canja DPO din ofishin ‘yan sanda dake cikin majalisa

Sace sandan ikon majalisa

Majiyar Daily Trust ta ce majiyarta ta tabbatar mata da cewa Sulu-Gambari ya kwashe kayan sa daga ofis, jiya, Asabar, ranar da takardar canjin aikin sa ta isa gare shi daga ofishin sakataren hukumar ‘yan sanda.

DUBA WANNAN: Shugaba Buhari zai mayar da hanakali kan magance wasu matsaloli biyu

Sulu-Gambari ya shaidawa kwamitin bincike na majalisar dattijai cewar ya kama mutum shida dangane da batun sace sandar majalisa da aka yi a watan Afrilu.

Saidai shelkwatar ‘yan sanda ta musanta cewar ta kama mutanen shidan ne saboda sace sandar majalisar kafin daga baya kwamishinan ‘yan sanda mai kula da sashen saka idanu, Abu Sani, ya shaidawa kwamitin binciken cewar wadanda ake zargin na tsarea ofishin hukumar ‘yan sanda na Abuja.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel