Tanko Yakasai ya ragargaji shugaba Buhari bisa wancakalar da tsarin karatun Almajiri da GEJ ya bullo da shi

Tanko Yakasai ya ragargaji shugaba Buhari bisa wancakalar da tsarin karatun Almajiri da GEJ ya bullo da shi

- Buhari na cigaba da shan suka daga 'yan adawarsa

- Wani tsohon dan siyasa daga Arewa ya ragargaje shi bisa kin dorawa akan tsarin da tsohon shugaban da yake goyon baya ya bullo da shi

Tsohon dan siyasa kuma uba a wannan kasa Tanko yakasai ya bayyana cewa yankin arewancin kasar nan na fuskantar kalubale tare da matsaloli ne sakamakon halin ko in kula da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ke yi game da tsarin karatun Almajirai wanda tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya aiwatar.

Tanko Yakasai ya ragargaji shugaba Buhari bisa wancakalar da tsarin karatun Almajiri da GEJ ya bullo da shi

Tanko Yakasai ya ragargaji shugaba Buhari bisa wancakalar da tsarin karatun Almajiri da GEJ ya bullo da shi

Yakasai ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da jaridar Punch ta yi da shi, ya ce “Akwai jami’o’in da tsohon shugaban kasa ya kirkira guda tara a yanki arewa, hudu kuma a yanki kudancin kasar nan kuma an kashe makudan kudade wajen samar da su, sai dai wannan gwamnatin bata kara waiwayarsu ba balle ta cigaba da habaka su ba”.

“Wannan shi ne abinda ya faru da tsarin karatun Almajiri wanda Jonathan ya kirkira, tsarin zai bawa kowane Almajiri dammar yin karatunsa na addini tare da kuma karatun boko a lokaci guda, sai dai har ya zuwa yanzu ba mu ga wani ynukuri daga wannan gwamnati ba wanda zamu iya cewa tana da ra’ayin cigabansa, wannan shi ne dalilin da yasa yankinmu na Arewa ke fuskantar matsaloli. Na kalubalanci duk wani da zai iya fitowa domin nuna wani cigaba da aka samu daga shekara ta 2015 zuwa yanzu akan tsarin karatun Almajiri face koma baya.”

KU KARANTA: Yan matan Dapchi da aka sace kwanan baya sun koma makarantar su ta da

Har way au, Tanko ya bayyana cewa cigaban da aka samu game da canjin kudaden kasar waje ya samo asali ne saboda tashin farashin mai a kasuwar duniya ba wai yunkurin gwamnati ba.

“Idan muka yi duba da kasashe irin su Indonesia da kasar Malaysia zamu ga cewa sun samu gagarumar nasara akan harkar da ta shafi man fetur da kuma Noma”, Yakasai ya bayyana.

“Amma gwamnatin Buhari babu wani abu da ta yi face shaci-fadi da kuma aringizon cigaba game da canjin kudade kasashen waje. Amma mu san cewar hakan ya samo asali ne a dalilin tashin farashin man fetur a kasuwar duniya ba wai yunkurin gwamnati bane”.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel