Annoba: Mutane na cigaba da kamuwa da Cutar Kwalara a Adamawa

Annoba: Mutane na cigaba da kamuwa da Cutar Kwalara a Adamawa

- Annobar Kwalara ta barke a jihar Adamawa, har ta fara mummunar barna

- Hukumar lafiya ta jihar Adamawa ta tabbatar da barkewar annobar Amai da Gudawa a jihar, inda mutane 434 suka kamu da cutar sai kuma mutane 13 ne suka rasa rayukansu a dalilin barkewar annobar.

Kamar yadda bayani yake fitowa daga bakin mai yaɗa labari na hukumar wato Abubakar Mohammed, ya tabbatar da faruwar hakan a wani jawabi da ya gabatar a yau Lahadi a garin Yola dake jihar ta Adamawa.

Annoba: Mutane na cigaba da kamuwa da Cutar Kwalara a Adamawa

Annoba: Mutane na cigaba da kamuwa da Cutar Kwalara a Adamawa

Inda ya bayyana cewa "Duk yawan wadanda suka kamu da annobar sun fito ne daga karamar hukumar Mubi ta Arewa da kuma Mubi ta Kudu, wanda jummular wanɗanda suka kamu da cutar a jiya 26 ga watan Mayu, suka kai 434 sai kuma wanda suka rasu har mutane 13".

Ya cigaba da bayani cewa "A ƙaramar hukumar Mubi ta Arewa an samu kaso 3.0% cikin 100 na waɗanda suka kamu da kuma 211 sai mutane 7 da suka rasu duk daga karamar hukuma. Ita kuwa karamar hukumar Mubi ta Kudu an samu kaso 2.7 cikin 100 na wanda suka kamu da adadin 223 sai mutane 6 da suka rasa rayukansu".

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Bayan Koriya ta lalata masana'antar nukiliyar, Trump ya janye daga ganawa da Kim Jong Un

Shugaban hukumar lafiya ta babban Asibitin garin Mubi wato, Dakta Ezra Sakawa yace yawancin waɗanda suka kamu da cutar dukkaninsu an ba su kulawa kuma da yawansu sun warke har an sallame su daga asibitin.

Annoba: Mutane na cigaba da kamuwa da Cutar Kwalara a Adamawa

Annoba: Mutane na cigaba da kamuwa da Cutar Kwalara a Adamawa

Idan ba a manta ba makonni biyu da suka wuce Legit.ng ta kawo muku rahotan labarin barkewar annobar Amai da Gudawa a garin na Mubi a sakamakon ta'ammali da gurbataccen ruwa da jama'ar yankin ke yi.

Kaso 90% na mutanen dake zaune a wannan yanki suna amfani da ruwa ne daga matatar Tuka-tuka wato (Boreholes) a Turance sai kuma ruwan kogin Yedzaram.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel