Yaki da cin hanci da rashawa a gwamnatin Buhari duk bi-ta-da-kulli ne - Sanata Baba Ahmed

Yaki da cin hanci da rashawa a gwamnatin Buhari duk bi-ta-da-kulli ne - Sanata Baba Ahmed

Fitaccen dan siyasar na dake zaman tsohon dan majalisar wakilai da kuma majalisar dattijai kuma dan asalin jihar Kaduna, Sanata Baba-Ahmad ya yi kaca-kaca da kurarin da gwamnatin shugaba Buhari ke yi na cewa tana yakar cin hanci da rashawa.

Sanatan a yayin wata fira da yayi da wakilin majiyar mu ta Daily Trust ya bayyana cewa yaki da cin hanci da rashawar da shugaban kasar ke wakar yana yi tamkar bita-da-kulli ne kawai domin cin zarafin wasu adawa da shi.

Yaki da cin hanci da rashawa a gwamnatin Buhari duk bi-ta-da-kulli ne - Sanata Baba Ahmed

Yaki da cin hanci da rashawa a gwamnatin Buhari duk bi-ta-da-kulli ne - Sanata Baba Ahmed

KU KARANTA: Rundunar sojin Najeriya ta 7 a Maiduguri tayi sabon shugaba

Legit.ng ta samu cewa da aka tambaye shi kuma ko me yasa yake neman takarar shugaban kasa a 2019, sai tsohon Sanatan ya bayyana cewa yana neman ya zama shugaban kasar Najeriya ne domin ya bayar da gudummuwar sa ga cigaban kasar musamman ma yanzu da gwamnatin shugaba Buhari ta lalata ta.

A wani labarin kuma, Yayin da batun takaddamar nan game da yadda tsohon shugaban kasar Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya kashe makudan kudade wajen inganta harkar wutar lantarkin kasar ke cigaba da wanzuwa, a jiya ya fitar da wani rahoton bincike da hukumar EFCC ta yi masa a lokacin mulkin marigayi shugaba Yar'adua.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel