Ranar yara: Shugaba Buhari ya aike da sakon sa zuwa ga jami'an tsaro

Ranar yara: Shugaba Buhari ya aike da sakon sa zuwa ga jami'an tsaro

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya kalubalanci dukkan jami'an tsaro, iyaye da ma shugabannin gargajiya da na addinai da su tashe tsaye wajen ganin sun tabbatar da kawo karshen cin zarafin yara kanana.

Shugaban kasar dai kamar yadda muka samu, yayi wannan kiran ne a cikin wani sakon da ya fitar ga manema labarai domin tunawa da ranar yara ta duniya da aka saba yi duk ranar 26 ga watan Mayu na shekara.

Ranar yara: Shugaba Buhari ya aike da sakon sa zuwa ga jami'an tsaro

Ranar yara: Shugaba Buhari ya aike da sakon sa zuwa ga jami'an tsaro

KU KARANTA: Garuruwa 7 da aka gano mai a yankin Arewa

Legit.ng ta samu cewa shugaban ya kuma kara da cewa maudu'in na wannan shekarar da aka sawa taken "Samar da kyakkyawan yanayi mai cike da tsaro domin yara: Hakki da ya rataya akan dukkanin mu ya dace sosai."

A wani labarin kuma, Sabanin ra'ayoyin mafiya yawan 'yan siyasa a jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya, daya daga cikin jiga-jiganta kuma gwamnan jihar Ebonyi, Mista David Umahi ya sha alwashin cigaba da girmama shugaban kasa Muhammadu Buhari duk kuwa da kasancewar su a jam'iyyu daban daban.

Gwamnan dai ya bayyana cewa shi fa shugaban kasar uban gidan sa ne kuma yana mutun ta shi tare da yin fashin bakin cewa ba dole bane sai ya ci zarafin shi sannan ne zai zama dan jam'iyyar PDP na hakika.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel