Shugaba Buhari ya bayyana wasu matsaloli biyu da zai mayar da hankali a kan su

Shugaba Buhari ya bayyana wasu matsaloli biyu da zai mayar da hankali a kan su

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jaddada niyyar gwamnatin tarayya na bayar da gudunmawa da goyon baya ga duk wasu kungiyoyi dake yaki da shan miyagun kwayoyi ,kalubalen da mata da kananan yara ke fama da shi, kuma tallafawa matasa.

Yayin wata ganawa da shugaba Buhari ya yi da matan gwamnoni a yau, Lahadi, a Abuja shugaba Buhari ya bayyana farincikin sa da shirye-shirye da matan gwamnonin ke bullowa das u a jihohin Najeriya 36 domin inganta rayuwar jama’a, musamman mata da matasa.

A ganawar sat a farko da matan gwamnonin tun bayan hawan sa karagar mulki, Buhari, ya ce ‘yan Najeriya na matukar godiya da irin kauna da kulawa da matan gwamnoni ke nunawa ga masu karamin karfi.

Shugaba Buhari ya bayyana wasu matsaloli biyu da zai mayar da hankali a kan su

Shugaba Buhari

Kazalika Buhari ya jinjina masu a kan yadda suke nuna kulawar su a kan mutanen dake zaune a sansanin ‘yan gudun hijira.

DUBA WANNAN: Ta tonu: Yadda majalisa da bangaren zartarwa suka yiwa talakan Najeriya yankan baya a mulkin Jonathan

Buhari ya shaidawa matan gwamnonin cewar umarnin da gwamnatin tarayya ta bayar a kan hana sarrafa da shigo da kodin kasar nan na daga cikin kokarin da gwamnati ke yi domin dakile yaduwar miyagun kwayoyi a tsakanin matasa.

A jawabin tan a maraba ga matan gwamnonin, uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta shaidawa shugaban kasa cewar, matan sun ziyarce shi ne domin sanar das hi irin kalubalen da suke fuskanta a kokarin sun a kawo karshen matsalar mata masu juna biyu da kananan yara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel