Majalisar wakilai ta mayar wa Okonjo Iweala raddi a kan karbar cin hancin biliyan N17bn

Majalisar wakilai ta mayar wa Okonjo Iweala raddi a kan karbar cin hancin biliyan N17bn

Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, Mista Femi Gbajabiamila, ya bayyana cewar bashi da masaniyar batun zargin karbar cin hancin kudi, biliyan N17bn, a shekarar 2015 kafin su amince da kasafin kudin da tsohon shugaban kasa ya gabatar gaban su.

A cikin littafin da ta wallafa mai taken “Fighting corruption is dangerous: The story behind the headline”’ Okonjo Iweala ta bayyana yadda ‘yan majalisun kasa suka dinga wahalar tare da karkatar da kudi masu dumbin yawa karkashin mulkin Jonathan.

Iweala ta bayyana yadda a shekarar 2015 shugabancin majalisar wakilai ya tilasta bangaren zartarwa biyan su zunzurutun kudi, biliyan N17bn, kafin su amince su zartar da kasafin kudin shekarar da shugaban kasa ya gabatar a gaban su.

Majalisar wakilai ta mayar wa Okonjo Iweala raddi a kan karbar cin hancin biliyan N17bn

Majalisar wakilai ta mayar wa Okonjo Iweala raddi a kan karbar cin hancin biliyan N17bn

Wannan kudi da Okonjo Iweala ke Magana basa daga cikin kudin kasafin biliyan N150 da ake warewa majalisun kasa domin gudanar da aiyukan su.

Gbajabiamila, shine shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, y ace dama Iweala tana jin haushin ‘yan majalisar wakilan tun lokacin da take minista.

DUBA WANNAN: Kurunkus: Gwamnatin tarayya ta fitar da sunayen wadanda suka saci kudin gwamnati lokacin mulkin PDP

Da yake kare abokan aikin sa, ‘yan majalisa, Gbajbiamila, ya bayyana cewar rashin daidaito a rabon aiyukan da gwamnatin tarayya zata yi ke saka ‘yan majalisar kokarin cusa nasu aiyukan a cikin kasafin kudin da ake gabatar masu.

Kazalika, wasu ‘yan majalisar biyu; Abdulmumin Jibrin da Sanata Eyinnaya Abaribe, sun musanta batun karbar wani cin hanci tare da bayyana cewar kudin ba aljihun ‘yan majalisa ya shiga ba, an kara su ne cikin kasafin kudin kasa bayan ‘yan majalisar sun kara wasu aiyuka da suka so a yi a mazaban su kasancewar shekarar 2015, shekarar zabe ce da kowanne dan siyasa ke son ya nuna aikin sa domin samun kuri’u.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel