Shugaba Buhari ya gana da Matan Gwamnonin Jihohin Najeriya a Fadar Aso Villa

Shugaba Buhari ya gana da Matan Gwamnonin Jihohin Najeriya a Fadar Aso Villa

- Shugaban kasa Buhari ya gana da Matan Gwamnonin Jihohi a jiya

- Masu dakin Gwamnoni su ka zanta da Shugaban Kasar a Fadar sa

- Aisha Buhari tana tare da sauran Iyalan Gwamnonin na Kasar su 36

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gana da Matan Gwamnonin Najeriya a fadar sa na Aso Rock a jiya Asabar da dare kamar yadda mu ka samu labari daga Hadiman Shugaban Kasar.

Shugaba Buhari ya gana da Matan Gwamnonin Jihohin Najeriya a Fadar Aso Villa

Muhammadu Buhari tare da Matan Gwamnonin Kasar nan

An yi ganawar ne a wani dakin taro da ke cikin Aso Villa a jiya 26 ga watan Mayu lokacin da aka sha ruwa. Kusan dai kaf Matan Gwamnonin Kasar nan 36 su na wajen wannan taron da aka yi da Shugaban Kasa Buhari.

Mai Girma Uwargidar Shugaban Kasar watau Hajiya Aisha Muhammadu Buhari tana cikin taron inda har Iyalan wasu Gwamnonin Kasar su ka mikawa Shugaban Kasa Buhari wasu kyaututtuka bayan an kammala taron.

KU KARANTA: Tsohon Shugaba Goodluck ya kai kokon barar sa wajen Shugaba Buhari

Shugaban Kasar dai ya ajiye banbancin Jam’iyya a gefe guda ya zanta da daukacin Iyalin Gwamnonin na Najeriya bayan anyi buda-bakin azumi. Daga cikin Gwamnonin akwai wadanda ke Jam’iyyar adawa na PDP da ma APGA.

Shugaban Kasar dai tun da ya hau mulki ya kan yi irin wannan liyafa ko buda-baki da Malamai ko ‘Yan Majalisa har da Musakai a fadar sa da lokacin azumin Watan Ramadan mai albarka.

Kun ji a jiya ne Gwamnatin ta Shugaban Kasa Buhari ta zayyano wasu kadan daga cikin gaban da aka samu a karkashin mulkin APC a bangaren tattalin arziki a shekarar da ta wuce ta 2017.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel