Dalilai 4 da suke sanya yawaitar fyade a kasar nan

Dalilai 4 da suke sanya yawaitar fyade a kasar nan

- Fyade wata mummunar ta’ada ce da ke kara yawaita a cikin al’umma duk kuwa da cewa Gwamnati da Malaman addini na iyakar kokarinsu wajen fadakarwa da kuma daukan matakan doka. Amma abin tambayar shi ne, menene dalilin da ya sanya fyaden ke kara ta’azzara?

- Wani shaharran Lauya daga jihar Fatakwal Mr Kingdom Ifedichukwuezi, ya lissafa wasu dalilai guda 4 da yake ganin sune musabbabi kuma kashin bayan yawaitar fyade a cikin al’umma.

1 shaye-shayen Muggan kwayoyi da kuma barasa

Giya dole ta zo a ta farko domin kuwa har kirari ake yi mata da kamru uwar laifi, in an shaki an bude kofar aikata duk wani laifi. Sannan kwayoyi na taka muhimmiyar rawa wajen lalatawa da kuma dagula tunanin masu ta’ammali da su, su aikata laifi kowanne iri ba tare da tunanin mai zaije ya komo ba. A cewar Lauyan zai yi wahala a samu wanda ya aikata laifin fyade ba tare da yayi ta’ammali da daya koma biyun daga ciki ba.

Abubuwa 4 da suka sanya yawaitar fyade da hanyoyin magance su

Abubuwa 4 da suka sanya yawaitar fyade da hanyoyin magance su

2 Shigar banza mai bayyana tsiraici

A wajen wasu Matan sanya kaya masu bayyana tsiraicin jikinsu shi ne kololuwar ado, a don haka mutukar kaya ba su bayyana surar jikinsu a waje ba to tamkar ba su hadu ba kenan. Sanya irin matsattsun kayan kan janyo hankalin Maza kansu wanda wasu lokutan har ta kai ga sun neme su da lalata idan sunki amincewa kuma sai su yi musu fyade ta karfi.

Abubuwa 4 da suka sanya yawaitar fyade da hanyoyin magance su

Abubuwa 4 da suka sanya yawaitar fyade da hanyoyin magance su

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya bayyana nasarorin da Gwamnatin sa ta samu shekarar da ta wuce

A cewar Lauyan idan da Matan zasu gane da sun hutar da kansu wajen sanya kayan da su kansu kan zame musu wahala, hakan zai sanya a rika girmama su domin sun kare mutuncinsu.

3 Muggan Abokai

Ifedichukwuezi ya ce, abin takaici ne ganin yadda har yanzu iyaye suka kasa yin komai wajen lura da wadanne abokai ‘ya’yansu suke hulda da su, domin a cewarsa hulda da lalatattun abokai ita ce hanya mafi sauki da za’a iya bi wajen sauyawa ‘ya’ya dabi’a wadda zata kaisu ta baro a mafi yawancin lokuta.

4 Gazawar Malaman Addini

Masallatai da kuma Coci-coci sun gaza wajen fadakarwa da kuma sauya tunanin mabiyansu sakamakon kumbiya-kumbiya da rashin fitowa fili su kalubalanci wannan ta’ada ta fyade.Domin a ganinsa inda ana samun hakan da tuni zai zamo a bin kunya a kama wani mabiyin Addini ya aikata laifin fyaden.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel