Ronaldinho: Karya ne ake yi min ba wasu mata biyu da zan aura

Ronaldinho: Karya ne ake yi min ba wasu mata biyu da zan aura

- Shahararren 'Dan kwallon kafar nan na kasar Brazil,Ronaldinho ya musanta labarin da ake yadawa na cewa zai auri mata biyu a lokaci daya

- A farkon makon nan ne, ake ta yadawa cewa tsohon tauraron kungiyar kwallon kafa ta Barcelona

- Ronaldo de Assis Moreira, ya shirya auren 'yammatan shi, Priscilla Coelho da Beatriz Souza a gidan shi a watan Augusta

Ronaldinho: Karya ne ake yi min ba wasu mata biyu da zan aura

Ronaldinho: Karya ne ake yi min ba wasu mata biyu da zan aura

Kamar yanda kafafen yada labarai na kasar Brazil suka ce, Tsohon Dan kwallon kafan na duniyan yana ba matan albashin pam 1,500. Kuma yana basu kyautuka iri daya.

SporTV kwanan nan tayi hira da tashar wasanni ta Brazil, Ronaldinho ya musa zancen auren. Yana cewa: "Duniya tana ta kirana. Bazan yi aure ba, wannan babbar karya ce."

DUBA WANNAN: Shugaba Buhari ya soke kwangilar da Amaechi ya baiwa yahudawan Israila

Duk da ma dai auren mata biyu haramun ne a kasar ta Brazil, in har akayi auren, Shahararren Dan kwallon kafar da matan biyu zasu fuskanci hukuncin shekaru 6 a gidan kaso.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel