Yankan baya: Ashe wasu manyan arewa suna can suna neman wanda zasu tsayar a matsayin shugaban kasa

Yankan baya: Ashe wasu manyan arewa suna can suna neman wanda zasu tsayar a matsayin shugaban kasa

Shuwagabannin Arewa da kuma masu ruwa da tsaki (NLSA) kungiya ce ta maza da mata yan arewa wadda take taka muhimmiyar rawa a siyasan ce, sunce sun kafata ne don taimakon yan arewa da kuma Najeriya baki daya.

Yankan baya: Ashe wasu manyan arewa suna can suna neman wanda zasu tsayar a matsayin shugaban kasa
Yankan baya: Ashe wasu manyan arewa suna can suna neman wanda zasu tsayar a matsayin shugaban kasa

Yanda yan arewa ke neman takarar shugaban kasa a boye.

Shugaban kungiyar Alhaji Tanko Yakasai yace badon shekarun sa ba daya maida NLSA abar kwatance a fadin kasar nan.

Bada dadewa ba suka kaiwa tsohon shugaban kasa Shehu Shagari ziyara tsohon shugaban soja, Ganar Ibrahim Badamasi Babangida, Ganar Yakubu Gawon da kuma tsohon Mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo, sunkai wannan ziyara ne a kokarin su na yada manufofin su ga yan Arewa.

Wani Memba na NLSA yace babu wani abun damuwa idan yan arewa suka taimaka wajen zabar shugaban kasa wanda bazaiji kunyar tunkarar matsalolin yan arewa ba.

Munyi ammana cewa muna fama da talauci musamman a arewacin kasar nan wannan shine abunda zamu fara yaki dashi, mun fara da shugabannin mu na arewa da zarar mun kammala zamu je Kudu suma mu basu shawara yanda Nageriya zata zame mana yanda mukeso.

Shin mun damu da zuwan 2019 ?Eh da A'a, Eh saboda kasancewar mu yan Nageriya saboda munason ci gaban kasar, A'a saboda ba'a sanyamu a ciki ba kuma ba mune hukumar zabe ba saidai kawai zamu kada kuri'a.

Wannan dalili ya sanya kungiyar take aiki tukuru tare da masu ruwa da tsaki na arewa wajen duba wanda zasu goyawa baya a lokacin zabe.

Samar da aikinyi ga matasan arewa yana daya daga cikin abunda kungiyar ke kokari akai.

NLSA tana goyon bayan wasu kungiyoyi na Kudu wajen kudirin su a 2019,tare da kuma alkawari na wata alfarma idan kujerar ta koma hannun su.

ADC, CNM tare da wasu sunyi wa tattaunawa hadin gwiwa wajen tsige APC.

A kokarin su tsige jam'iyar APC da kuma kawo karshen mulkin shugaban kasa Muhammad Buhari a 2019.CNM da ADC. Mai magana da yawun CNM yace Chief Olusegun Obasanjo ya mike kafa yana sauraran komawar Buhari Daura a 2019.

DUBA WANNAN: Abubuwan da shugaba Buhari yayi a 2015-2018

A wannan shiri jam'iya daya zasu tsayar da dan takarar shugaban kasa yayin da daya kuma zasu tsayar da mataimaki. Tuntuni dai Obasanjo yace zaiyi magana da dan takarar shugaban kasa don yayiwa wannan tafiya mubaya'a.

Shin abubuwa zasu tafi yanda aka tsara? Yana da matukar wahala Buhari ya koma a 2019.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel