Wani Mahaifi ya shiga hannu da laifin yiwa 'Ya'yan sa Mata 4 Fyade a garin Fatakwal

Wani Mahaifi ya shiga hannu da laifin yiwa 'Ya'yan sa Mata 4 Fyade a garin Fatakwal

Wani Mummunan rahoto da jaridar The Punch ta ruwaito ya bayyana cewa, a ranar Alhamis din da ta gabata ne wani Mahaifi mai shekaru 41 a duniya, Michael Akpan, ya gurfana a gaban kotun Majistire da laifi yiwa 'ya'yan sa mata 4 fyade.

Rahoton da jaridar ta ruwaito a ranar Alhamis din da ta gabata ya bayyana cewa, akwai yiwuwar wannan mahaifi ya yanki tikitin zama a gidan wakafi har na tsawon abinda ya rage na rayuwar sa sakamakon girman laifi da ya aikata.

Kotun tana zargin Akpan da laifin yiwa 'ya'yan sa mata 4 ta karfi wajen murkushe su domin dauke yunwa da kwazabar sa mai muni ta da namiji.

Laifin da Akpan ya aikata a yankin Borokiri dake birnin Fatakwal na jihar Ribas yayi matukar muni kamar yadda Alkaliyar Kotun, Zinnah Alikor ta bayyana.

Wani Mahaifi ya shiga hannu da laifin yiwa 'Ya'yan sa Mata 4 Fyade a garin Fatakwal

Wani Mahaifi ya shiga hannu da laifin yiwa 'Ya'yan sa Mata 4 Fyade a garin Fatakwal
Source: Twitter

Rahotanni sun bayyana cewa, wani da ga wannan shu'umin mutum, Fortune Ndah, shine ya cafke mahaifin nasu yayin da yake aikata alfasha da 'yan uwan sa mata hudu masu shekaru 2, 7, 11 da kuma budurwa 'yar shekaru 17 a duniya.

KARANTA KUMA: Mata 'Yan Majalisa na kawo barazana ga Kujerar Osinbajo - Buhari

A yayin da ba bu wani lauya mai kare Akpan a gaban kotu sakamakon girman laifin sa, bincike da sanadin dan da haifa ya tabbatar da cewa wannan babban laifi shine abinda ya saba aikatawa tun shekaru uku da suka gabata.

A na ta bangaren, Misis Zinna ta tuhumi mahaifiyar wannan yara dangane da rashin gano wannan kazanta da ake tafkawa akan 'ya'yayen ta du da cewar zaluncin Akpan ya tauye mata hakkin ta na kusantuwa da su ballantana sanin halin da suke ciki.

Alikor ta bayar da umarni na ci gaba da tsare Akpan a gidan maza yayin da za ta mika wannan lamari zuwa cibiyar zartar da hukunci ta jihar domin jin ta bakin ta, inda ta ce a halin yanzu kotun ba ta hurumin zartar da hukunci akan wannan lamari mai kunshe da bakin ciki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel