Raddi: Jonathan ne ya mayar da Najeriya abin dariya a idanun duniya - Fadar shugaban kasa

Raddi: Jonathan ne ya mayar da Najeriya abin dariya a idanun duniya - Fadar shugaban kasa

A yau Asabar ne fadar shugaban kasa ta bayyana cewa gwamnatin jam'iyyar PDP karkashin jagorancin tsohon shugaba Goodluck Jonathan janyo tabarbarewar abubuwa a kasar kana ta mayar da ita abin dariya tsakanin kasashen duniya.

Wannan mayar da martanin na zuwa ne bayan wasu kalamai da aka ruwaito cewa Jonathan ya fadi idan ya ke cewa ya jin kunyar yadda sauran kasashe ke ambaton Najeriya don bayar da misalin kasashen da al'amuran suka tabarbare.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa shugaba Jonathan ya ce Najeriya ta shiga cikin kasashen da ake nuni da su idan ana batun abubuwa marasa kyau a yayin da ya ke kaddamar da wata gada da gwamna Ayodele Fayose na jihar Ekiti ya gina a Ado Ekiti.

Fadar shugaban kasa ta mayar wa Jonathan martani a kan sukar da ya yi wa APC

Fadar shugaban kasa ta mayar wa Jonathan martani a kan sukar da ya yi wa APC

KU KARANTA: Yadda gwamnati ta bawa 'yan majalisa toshiyar N17bn kafin suka amince da kasafin kudin 2015 - Okonjo-Iweala

Jonathan ya kawo misalin inda aka ce wai shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo ya yi shagude kan yadda yanayin tsaro ya tabarbare a Najeriya da kuma faduwar darajar naira. An ruwaito ya ce "Ghana ba kamar Najeriya bane inda shanu ke yawo a kan tituna"

Jonathan ya ce ya ji kunya sosai a matsayinsa na tsohon shugaban kasa bayan ya saurari shugaban kasar da muke makwabtaka da ita yana ambatan Najeriya wajen nuni da abu mara kyau.

Sai dai fadan shugaban kasar ta bukaci Jonathan ya bawa gwamnatin shugaba Buhari sarari ta gyara barnar da gwamnatinsa ta tafka.

Mai magana da yawun shugaban kasa Malam Shehu Garba ya ce Najeriya ta kasance saniyar ware ne a karkashin mulkin Jonathan amma a yanzu mutuncinta ya fara dawowa.

Shehu Garba kuma ya kara da cewa idan wasu kasashen na yiwa Najeriya dariya, tabbas gwamnatin tsohon shugaba Jonathan ne ta janyo hakan. Ya kuma ce Najeriya na dawo da kimar ta a idanun duniya domin ko matafiya suna shaida hakan idan sun fita kasashen ketare.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel