Sauya sheka daga APC: Shehu Sani ya mayar da martani

Sauya sheka daga APC: Shehu Sani ya mayar da martani

Sanata Shehu Sani ya mayar da martani kan rahotannin da ke cewa shi da takwararsa, Suleiman Hunkuyi, na shirin sauya sheka daga jam'iyyar All Progressives Congress, APC, sanadiyar rikicin da ke faruwa a shiyar jam'iyyar na jihar Kaduna.

A martanin da yayi ta shafinsa na Facebook yace: " Da farko sune Shehu Sani ya koma PDP, sai suka ce Shehu Sani ya koma PRP, sannan Shehu Sani ya koma SDP, sai kuma Shehu Sani na shirin na shirin fita. Shehu Sani da safe, Shehu Sani da rana, Shehu Sani da yamma. Karamin shugaban kama karya da karnukansa kullin cikin tsoron suke ne?

"ZAN YI TAKARA, KUMA ZAMU HADU A FINAL INSHA ALLAH. "RONALDO da MESSI da SUAREZ da NEYMAR da PIERRE EMERICK da DANI CARVAJARL da LEONARDO BONUCCI da SALAH da ALEXIS SANCHEZ da SERGIO RAMOS da EDEN HARZARD da DAVID DE GEA da PAUL POGBA...Duk suna tare Damu su kuwa sai yan’daba da sojojin baka".

KU KARANTA: Shehu Sani da Hunkuyi suna gab da ficewa daga jam'iyyar APC, sun fadi dalilansu

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa Wata bangare na jam'iyyar APC da ke karkashin jagorancin Sanata Suleiman Hunkuyi da ke wakiltan Kaduna ta arewa da Sanata Shehu Sani mai wakiltan Kaduna ta tsakiya sunce akwai yiwuwar za su fice daga jam'iyyar.

Shugaban kungiyar, Tom Maiyashi, wanda ya fitar da sanarwan ya ce akwai wasu abubuwa guda biyu da suka faru a jihar wanda suka tabbatar masa da cewa babu shugabanci na gari a jam'iyyar APC reshen jihar Kaduna kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel