Muslmai a Najeriya sun gudanar da zanga-zangar kin jinin Isla'ila

Muslmai a Najeriya sun gudanar da zanga-zangar kin jinin Isla'ila

Wasu al'ummar musulmi a jihar Oyo dake shiyyar kudu maso yammacin Najeriya a ranar Juma'ar da ta gabata sun gudanar da zanga-zangar kin jinin kasar Isra'ila a kan cigaba da mamayar da take yi wa yankin kasar Falasdinawa.

Da yake magana game da musabbabin yin zanga-zangar, shugaban gamayyar kungiyoyin musulmin kuma shugaban kungiyar gidauniyar Al-Qudus Malam Atta Rasheed ya bayyana cewa abun takaici ne yadda kasashen duniya suka zura ido suna kallon rashin adalcin mamayar tun shekarar 1948.

Muslmai a Najeriya sun gudanar da zanga-zangar kin jinin Isla'ila

Muslmai a Najeriya sun gudanar da zanga-zangar kin jinin Isla'ila

KU KARANTA: Muna daf da hadewa da wasu jam'iyyu don korar APC - PDP

Legit.ng ta samu cewa daga nan ne kuma sai Malam Atta ya bukaci dukkan mutanen duniya masu son zaman lafiya da su tashi tsaye wajen ganin sun yi tofin Allah-tsine ga mamayar domin kawo karshen cin zarafin da ake yi wa 'yan Falasdiwan.

A wani labarin kuma, mun samu cewa an samu wata mata mai suna Maria de la Luz a kasar Mexico mai shekaru 70 a duniya da ta ce tana dauke da ciki wata shidda.

Da take zantawa da majiyar mu a garin nata, tsohuwar da yanzu haka take jiran haihuwar dan ta na takwas ta ce ta tabbatar da shigar cikin na ta ne biyo bayan sakamakon hoton cikin da ta yi aka kuma fada mata cewa mace ce za ta haifa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel