Ina jin kunyar yadda sunan Najeriya ya baci a idanun duniya - Jonathan

Ina jin kunyar yadda sunan Najeriya ya baci a idanun duniya - Jonathan

Tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Ebele Jonathan ya bayyana takaicin sa akan yadda yace wasu bata gari 'yan asalin kasar nan suka bata sunan kasar a idanun duniya ta hanyar aikata munanan laifuka.

A kokarin sa na yin karin bayani game da hakan, Goodluck Jonathan ya bayar da misalin yadda yace shugaban kasar Ghana Nana Akufo Addo ya yi anfani da kasar ta Najeriya wajen bayyana yadda harkoki ke cigaba da tabarbarewa musamman ma a fannonin tsaro da tattalin arziki.

Ina jin kunyar yadda sunan Najeriya ya baci a idanun duniya - Jonathan

Ina jin kunyar yadda sunan Najeriya ya baci a idanun duniya - Jonathan

KU KARANTA: An bukaci Buhari yayi murabus

Legit.ng ta samu cewa Jonathan yayi wannan tsokacin ne yayin da yake gabatar da jawabin sa lokacin kaddamar da wata katafariyar gada a jihar Ekiti da gwamnan jihar Ayodele Fayose ya gina.

A wani labarin kuma, Tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Ebele Jonathan mun samu cewa ya shawarci shugaban kasar Najeriya mai ci a yanzu Muhammadu Buhari da kar ya yi anfani da karfin mulkin sa wajen tankwara zaben jihar Ekiti da za'a gudanar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel