Wata rigimamiyar mata ta kaiwa alkali farmaki a kotu yayin da ake zaman shari'a

Wata rigimamiyar mata ta kaiwa alkali farmaki a kotu yayin da ake zaman shari'a

Hukumar Yan sandan jihar Legas ta gurfanar da wata mace mai suna Alexia Thomas gaban wata kotun majisatre da ke Igbosere inda ake zarginta da kaiwa wani babban alkali farmaki.

Rahotanni sun bayyana cewa matar ta haddasa tashin hankali a harabar kotun yayin da alkali ke sauraon shari'a kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

An gano cewa babban alkalin da ya bukaci a sakaya sunansa ya aike wa matar sammaci amma ta ki amsawa inda ta ce ita bata san shi ba saboda haka ba za ta amsa kirar da kotun ke yi mata ba.

Wata rigimamiyar mata ta kaiwa alkali farmaki a kotu yayin da ake zaman shari'a

Wata rigimamiyar mata ta kaiwa alkali farmaki a kotu yayin da ake zaman shari'a
Source: Twitter

Majiyar Legit.ng ta gano cewa rikicin ya balle ne tsakanin Thomas da dan sanda mai shigar da kara wanda ya yi yunkurin kama ta saboda an bayar da belinta amma bata dawo ba.

KU KARANTA: Wata mace ta kwancewa mijinta zani a kotu, ta kuma bukaci a raba aurensu

A bayar da rahoton cewa an gurfanar da ita a gaban kotu ne a shekarar 2017 bisa wasu laifuka uku amma bayan an bayar da belinta sai ta ki dawowa domin a cigaba da sauraron shari'ar ta.

Dan sandan ya yi ta neman ta amma bai same ta sai kwatsam ya hadu da ita a harabar kotun a ranar 17 ga watan Mayu inda ya nemi kama ta amma tayi ta masa kururuwa wanda hakan ya kawo cikas ga shari'ar da akeyi a kotun.

Hakan yasa Alkalin kotun ya umurci a gabatar da ita gaban kotun amma ta ki amsawa inda da ce ba abinda ya dameshi da ita sai dai alkalin ya saka an damke ta inda aka gurfanar da ita bisa laifin tayar da zaune tsaye.

A cewar dan sanda mai shigar da kara, Saja Friday Mammeh, laifukan da ake tuhumar matar dashi sun sabawa sashi na 104(1) (a) da kuma 168(d) na dokar masu aikata laifuka na Jihar Legas ta shekarar 2015.

Sai dai har ila yau matar da musanta aikata laifin da ake tuhumar ta dashi kuma an bayar da belinta kan kudi N250,000 tare da mutum daya da ya tsaya mata. An dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 20 ga watan Yunin 2018.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel