Oshiomole ya ce PDP ce ta tsiyatar da Najeriya, ya bayar da dalilansa

Oshiomole ya ce PDP ce ta tsiyatar da Najeriya, ya bayar da dalilansa

Tsohon gwamnan jihar Edo, Kwamared Adams Oshiomole ya sake yiwa gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan shagude inda ya ce idan da za'a rabawa dukkan 'yan Najeriya kudaden da ake zargin gwamnatin Jonathan ta karkakatar da kowa ya zama attajiri.

Dama tun a baya, Oshiomole ya dade yana cacakar gwamnatin Jonathan a kan zargin karkatar da kudaden Najeriya.

Oshiomole ya yi wannan furuci ne a jiya Juma'a yayin da ya ke jawabi ga shugabanin jam'iyyar APC na jihar Edo.

Aljihun kowane 'dan Najeriya zai cika ya batse idan da za'a raba musu da aka karkatar zamanin Jonathan - Oshiomole

Aljihun kowane 'dan Najeriya zai cika ya batse idan da za'a raba musu da aka karkatar zamanin Jonathan - Oshiomole

Tsohon shugaban kungiyar kwadago na kasan, ya ce dole ne a rika jadada irin mulkin da gwamnatin PDP ta kwashe shekaru 16 tana yi wanda hakan ne ya jefa Najeriya cikin talauci da fatara.

KU KARANTA: Yadda gwamnati ta bawa 'yan majalisa toshiyar N17bn kafin suka amince da kasafin kudin 2015 - Okonjo-Iweala

Ya ce jam'iyyar APC a karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ta na kokoarin ceto yan Najeriya daga cikin halin kuncin da PDP ta jefa kasar.

"Hakkin mu ne magoya bayan jam'iyya mu fadakar da mutanen karkara wadanda suka jefa mu irin halin da muka shiga a yau da kuma kokarin da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari keyi don ceto mu wanda hakan yasa yan Najeriya a yanzu sun fara alfahari da kasar," inji Oshiomole.

Tsohon gwamnan ya cigaba da cewa ya kamata mutane su fahimci irin wahalar da ke tattare da yin gyara a gidan da ya ruguje saboda daura turbar sabon gini da kammala ginin ba abu ne da za'a iya kammalawa a dare daya ba.

A cikin yan kwanakin nan ne Oshiomole ya nuna sha'awarsa na tsayawa takarar kujeran shugabancin jam'iyyar APC inda kuma ya kara da cewa shugaba Buhari ne zai lashe zabe saboda irin nasarorin da ya samu a yanzu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel