Jami'in Kwastam ya harbe Dattijo mai shekaru 70 daga shiga sulhunta sabani a jihar Oyo

Jami'in Kwastam ya harbe Dattijo mai shekaru 70 daga shiga sulhunta sabani a jihar Oyo

Majiyar mu ta samu rahoton cewa, wani jami'in hukumar kwastam ya harbe wani dattijo har lahira yayin da ya shiga sulhunta sabani tsakanin fusatattun jami'an da wasu matasa.

Wannan lamari dai ya jefa iyalan wannan dattijo, Lamide Oke cikin halin kakanikayi, wanda ya kasance manomi a kauyen Olorunda na jihar Oyo.

Kamar yadda jaridar The Punch ta bayyana, wannan dattijo ya gamu da ajalin sa a hannun wani dan bindiga dadi cikin jami'an hukumar kwastam da ya harbe shi a yayin shiga sulhunta sabani dangane da gitta itace da wasu matasan kauyen suka yi.

Rahotanni sun bayyana cewa, al'ummar kauyen sun saba gitta manyan itace a gefen hanya sakamakon tsala gudu da masu ababen hawa ke yi yayin bibiyar hanyar, wanda hakan zai taimaka wajen sassauta afkuwar hadurra yayin guje-guje.

Jami'in Kwastam ya harbe Dattijo mai shekaru 70 daga shiga sulhunta sabani a jihar Oyo

Jami'in Kwastam ya harbe Dattijo mai shekaru 70 daga shiga sulhunta sabani a jihar Oyo

A yayin da marigayi Lamidi da dan uwansa Murtala mai shekaru 66 a duniya ke kan hanyar su ta dawowa daga na duke tsohon ciniki, jami'an na kwastam sun umarci Murtala akan kawar da wannan itatuwan daga hanya.

Budar bakin Murtala sai kwatsam yace sai dai su sauka daga motar su ta hawa su kawar da kansu kana su wuce, wanda wannan furuci ya fusata jami'an da har suka sauko da ga motar su kirar Hilux.

KARANTA KUMA: Uwar gidan Fani-Kayode ta haifi 'yan 3 reras

A sanadiyar haka ne fusatattun matasan kauyen da jami'an na kwastam suka fara cacar baki da har ta kai ga sautin harsashi ya fara fita, inda maraigayi Lamidi ya shiga sulhunta wannan sabani da ashe ajali ke kira.

Da yake shaidawa manema labarai kanin rahoton, Murtala ya bayyana cewa wani jami'i guda ne ya harbe dan uwan sa a kirji a yayin da yake kokarin bayar da baki da fusatattun ma'aikatan, inda kuma suka kama gaban su ba tare da waiwaye ba.

Kakakin hukumar 'yan sanda na reshen, Adekunle Ajisebutu, ya tabbatar da afkuwar wannan lamari inda kakakin hukumar kwastam na jihar, Abdullahi Lagos-Abiola, ya bayar da tabbaci akan korafin da hukumar 'yan sanda ta shigar dangane da lamarin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel