Yadda gwamnati ta bawa 'yan majalisa toshiyar N17bn kafin suka amince da kasafin kudin 2015 - Okonjo-Iweala

Yadda gwamnati ta bawa 'yan majalisa toshiyar N17bn kafin suka amince da kasafin kudin 2015 - Okonjo-Iweala

- Tsohuwar ministan kudi Ngozi Okonjo-Iweala ta fallasa yada majalisar kasa ta tilastawa fadar shugaban kasa ware musu N17bn kafin su amince da kasafin kudin 2015

- Tsohuwar ministan ta ce shugabanin majalisar sunyi amfani da kwamitoci daban-daban don karkatar da kudaden kasafin kudin zuwa aljihunansu

- Ta ce yan majalisar sun kirkiro da karin N20bn a matsayin kudin zabe na shekarar 2015 wanda daga baya suke rage zuwa N17bn kafin suka amince da kasafin kudin

Tsohuwar Ministan kudi, Ngozi Okonjo-Iweala ta yi tonon silili a kan yadda majalisar Najeriya ta tilastawa gwamnatin tarayya ware musu wasu kudade kafin su amince da kasafin kudin 2015 a zamanin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Ta fito fili: Dubi makuden kudin da gwamnatin Jonathan ta bawa yan majalisa kafin su amince da kasafin kudin 2015

Ta fito fili: Dubi makuden kudin da gwamnatin Jonathan ta bawa yan majalisa kafin su amince da kasafin kudin 2015

A sabuwar littafin da ta wallafa a kan gwagwarmayar yaki da rashawa mai suna 'Fighting Corruption is Dangerous: The Story Behind the Headlines', Iweala ta bayar da labarin yadda Majalisar tarayya ta tursasawa gwamnatin tarayya ware musu N17bn kafin suka amince da kasafin kudin 2015 kamar yadda The Nation ta ruwaito.

KU KARANTA: Rikicin IGP da Saraki: Abinda da shugaba Buhari ya fadawa Sanatoci da suka kai kara wajensa

Majiyar Legit.ng ta gano cewa tsohuwar ministan ta ce wannan abin ya faru ne a lokacin da farashin gangan danyem man fetur na fadi warwas a kasuwanin duniya inda kuma ta kara da cewa sun karbi wannan N17bn duk da cewa akwai wata N150 biliyan da aka saba ware wa majalisar don gudanar da harkokinta.

Iweala ta kara da cewa yana da matukar wahala yadda kasafin kudin zai je gaban kwamitoci da dama wanda galibinsu suna kokarin kirkiro wasu sabbin ayyuka ne ko kuma yin kari ga wasu ayyukan wanda hakan yana kawo cigas ga kasafin kudin.

Ta kuma bayyana yadda yan majalisar a kowane lokaci kokarinsu shine yadda za su yi kari kan adadin kudin da ake ware wa majalisar duk da cewa an ware musu 16% na dukkan kasafin kudin kasar.

Tsohuwar ministan ta bayyana yadda yan majalisar suka tubure wajen kin rage wasu daga cikin alawus dinsu duk da cewa a wannan lokacin farashin mai ya karye a kasuwannin duniya kuma abinda ya dace suyi kenan.

Iweala ta ce harka da yan majalisar abu ne mai matukar wahala duk da cewa ba dukkansu ne ke goyon bayan irin yadda majalisar ke kokarin azirta kansu ko da kuwa babu kudi a kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel