Rikicin IGP da Saraki: Abinda da shugaba Buhari ya fadawa Sanatoci da suka kai kara wajensa

Rikicin IGP da Saraki: Abinda da shugaba Buhari ya fadawa Sanatoci da suka kai kara wajensa

- Wasu sanatoci sun ziyarci shugaba Buhari a fadar sa inda suka bukaci ya shiga tsakanin IGP Idris Ibrahim da Bukola Saraki

- Shugaba Buhari ya fada musu cewa abinda yafi dacewa shine a bar kowa ya yi aikinsa kamar yadda doka ya tanada

Shugaba Muhammadu Buhari ya shaidawa yan majalisar da suka ziyarce shi don ya shiga tsakani ya sasanta Sufetan Yansanda, Ibrahim Idris da Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki cewa a bar kowace bangaren gwamnati tayi aikinta kamar yadda doka ta tanadar.

Shugaban kasan da ya zanta da sanatocin na tsawon mintuna biyar ya jadada musu cewa ya yi imani da cewa a bar kowa ya yi aikinsa ba tare da yi masa katsalandan ba lamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Rikicin IGP da Saraki: Abinda da shugaba Buhari ya fadawa Sanatoci da suka kai kara wajensa

Rikicin IGP da Saraki: Abinda da shugaba Buhari ya fadawa Sanatoci da suka kai kara wajensa

KU KARANTA: Shehu Sani da Hunkuyi suna gab da ficewa daga jam'iyyar APC, sun fadi dalilansu

A ranar Talata ne dai wata tawaga daga majalisar dattawa ta ziyarci Shugaban kasan a fadar Aso Villa inda ta gabatar da korafin Saraki na cewa Sufeta Idris ya mayar da yan kungiyar asirin da ake yiwa tambayoyi a jihar Kwara zuwa Abuja ne don ya yiwa Saraki sharri.

Jagoran tawagar, Sanata Ahmad Lawan (APC, Yobe) ya shaidawa manema labarai a karshen ganawar cewa shugaba Buhari ya ce yana sane da abubuwan da ke faruwa kuma zai dauki matakin da ya dace a kan lamarin.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa shugaban kasan ya yi wa tawagar bayanin yadda bangaren zartarwa a gwamnatin da ta shude ta rika tsoma hannu cikin harkokin sauran bangarorin gwamnati ya janyo fanin shari'a ta gaza yin aikin ta.

Majiyar har ila yau ta ce, shugaban kasan ya yi magana a kan darussan da ya koya a lokutan da ya tafi kotu a kan batutuwan zabe, hakan yasa ya ce ba zai tsoma hannunsa a harkokin sauran bangarorin gwamnati ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel