Shehu Sani da Hunkuyi suna gab da ficewa daga jam'iyyar APC, sun fadi dalilansu

Shehu Sani da Hunkuyi suna gab da ficewa daga jam'iyyar APC, sun fadi dalilansu

Wata bangare na jam'iyyar APC da ke karkashin jagorancin Sanata Suleiman Hunkuyi da ke wakiltan Kaduna ta arewa da Sanata Shehu Sani mai wakiltan Kaduna ta tsakiya sunce akwai yiwuwar za su fice daga jam'iyyar.

A wata sanarwa da suka fitar a ranar Juma'a, yan arewa din da ke kiran kansu da suna APC Akida sunce sun kammala bita a kan jam'iyyar da matsalolin shugabancin da ke adabar jam'iyyar a jiha da ma kasa kuma suna tunanin ficewa daga jam'iyyar da suka taimaka wajan kafawa.

Abin ya zo: Hunkuyi da Shehu Sani suna gab da ficewa daga jam'iyyar APC

Abin ya zo: Hunkuyi da Shehu Sani suna gab da ficewa daga jam'iyyar APC

APC Akida ta ce za ta dauki matakin ficewa ne "Idan babu wata kwakwarar alamar samun nasara wajen magance matsalolin wariyar da kuntatawa da akeyiwa wasu yan jam'iyyar a jihar Kaduna"

KU KARANTA: Gwamnatin Jihar Ekiti tayi wa tsohon shugaba Jonathan wata babban karamci

Shugaban kungiyar, Tom Maiyashi, wanda ya fitar da sanarwan ya ce akwai wasu abubuwa guda biyu da suka faru a jihar wanda suka tabbatar masa da cewa babu shugabanci na gari a jam'iyyar APC reshen jihar Kaduna kamar yadda The Cable ta ruwaito.

"Yadda aka gudanar da zabukan shugabanin jam'iyya da kuma zabukan kananan hukumomi a jihar ya tabbatar min da cewa rashin jagoranci mai kyau zai dushe duk wata farin jini da jam'iyyar ke dashi a jihar.

"Dama dai kungiyar APC Akida ta bayyana yiwuwar faruwar hakan tun da fari lokacin da ta lura da irin kamun ludayin gwamna Nasir El-Rufai," a cewar Maiyashi.

A saboda wannan dalilan ne kungiyar ke kira ga duk wadanda gwamna El-Rufai ke ganin girmansu da su hanzarta jan kunnensa domin kare jam'iyyar daga fadawa cikin bala'i. Kungiyar kuma ta sanar da mahukuntar jam'iyyar a jiha da kasa cewa za su fice daga jam'iyyar idan har ba'a yi gyara ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel