Majalisar dattawa ta sanya baki ta nemi kawo karshen yajin aikin ma’aikatar lafiya

Majalisar dattawa ta sanya baki ta nemi kawo karshen yajin aikin ma’aikatar lafiya

Majalisar dattawa ta shiga tsakani akan lamarin yajin aikin kungiyar ma’aikatan lafiya na JOHESU.

Shugaban majalisar dattawan, Bukola Saraki ya gana da ministan Kiwon Lafiya Isaac Adewole da na kwadago Chris Ngige, gami da shugabannin Kungiyar ma’aikatan jinya da na asibitocin kasar nan domin tattauna yadda za a kawo karshen yajin aikin da JOHESU suka shiga tun a watan Afrilu.

Saraki ya ce za su cigaba da tattauna wa da JOHESU da ministocin har sai an shawo kan matsalar.

Majalisar dattawa ta sanya baki ta nemi kawo karshen yajin aikin ma’aikatar lafiya

Majalisar dattawa ta sanya baki ta nemi kawo karshen yajin aikin ma’aikatar lafiya

Idan ba a manta ba ana nan ana ta kai ruwa rana tsakanin kungiyar JOHESU da gwamnatin tarayya, inda ita kungiya ke neman lallai sai a inganta wa ma’aikatan asibiti albashi da sauran alawus-alawus kamar yadda likitoci ke morewa a kasar nan.

KU KARANTA KUMA: Zamu bayyana yadda PDP ta sace kudaden Najeriya ta jefa talakawa cikin talauci - Oshiomhole

Hakan dai ya durkusar da ayyukan asibitocin kasar nan inda kullum kara tabarbarewa ya ke yi.

Gwamnati sun kasa gano bakin zaren.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel