2019: Jam’iyyu sun bullo da sababbin ka’idojin zabe

2019: Jam’iyyu sun bullo da sababbin ka’idojin zabe

- Gabanin zaben 2019, jam’iyyun siyasa da aka yiwa rajista 68 a fadin kasar, a ranar juma’a, a birnin tarayya suka sanya hannu a wasu sababbin ka’idoji na dokar zabe

- Cigaban ya samo asali ne daga taron farfado da ka’idojin jam’iyyun siyasar Najeriya da aka gudanar a birnin tarayya na kwanaki biyu

- Babban jami’in kungiyar jam’iyyun kasar NIPSS-PPLPDC, Farfesa Habu Galadima, yace ka’idojin sun tabbata ne bayan dubawar da masana suka yi akansu kafin kaddamar dasu ga jam’iyyun

Gabanin zaben 2019, jam’iyyun siyasa da aka yiwa rajista 68 a fadin kasar, a ranar juma’a, a birnin tarayya suka sanya hannu a wasu sababbin ka’idoji na dokar zabe.

Cigaban ya samo asali ne daga taron farfado da ka’idojin jam’iyyun siyasar Najeriya da aka gudanar a birnin tarayya na kwanaki biyu, wanda kungiyar jagorancin jam’iyyun siyasar (PPLPDC) ta makarantar dokoki da tsare-tsare ta kasa (NIPSS) ta shirya.

Babban jami’in kungiyar jam’iyyun kasar NIPSS-PPLPDC, Farfesa Habu Galadima, yace ka’idojin sun tabbata ne bayan dubawar da masana suka yi akansu kafin kaddamar dasu ga jam’iyyun su kuma amince dasu.

2019: Jam’iyyu sun bullo da sababbin ka’idojin zabe

2019: Jam’iyyu sun bullo da sababbin ka’idojin zabe

Galadima yace ka’idojin zasu kasance akan dokoki da aka shirya domin jam’iyyun siyasa da kuma mabiyansu su san yadda zasu gudanar da al’amurransu na zabe.

Abaya Legit.ng ta rahoto cewa Gwamnatin tarayya ta bayyana ranar Talata, 29 ga watan Mayu, a matsayin ranar hutun ma’aikata, domin bikin murnar ranar damokradiyya na shekarar 2018.

KU KARANTA KUMA: Hukumar EFCC ta tsare tsohon gwamnan jihar Kaduna Ramalan Yero har na tsawon sa’o’i 4 akan N700m na kudin kamfen

Ministan al’amuran cikin gida Abdurrahman Dambazau, ya bayyana haka a ranar juma’a, a birnin tarayya a mamadin gwamnatin tarayya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel