Gwamnan Bauchi ya bayyana dalilin da yasa mataimakinsa ya ajiye aiki

Gwamnan Bauchi ya bayyana dalilin da yasa mataimakinsa ya ajiye aiki

- Gwamnan jihar Bauchi Mohammed Abubakar a ranar juma’a ya bayar da haske akan dalilin da yasa mataimakinsa Nuhu Gidado ya ajiye aiki a ranar Laraba

- Gwamnan Abubakar ya bayyanawa manema labarai bayan sun gama sallar juma’a tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari, a fadar shugaban kasar, yace Gidado da sauran mutane da suka ajiye aiki sunyi haka ne don basu iya yin aiki da canjin dayazo dashi

- Gidado a takardar da ya rubuta ta ajiye aiki ya bayyana cewa cigaba da aiki ba alkhairi bane da adalci a tsakaninsa da gwamnan

A ranar Juma'a, 25 ga watan Mayu, Gwamnan jihar Bauchi Mohammed Abubakar ya bayar da karin haske akan dalilin da yasa mataimakinsa Nuhu Gidado ya ajiye aiki a ranar Laraba.

Gwamnan Abubakar ya bayyanawa manema labarai bayan sun gama sallar juma’a tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari, a fadar shugaban kasar, cewa Gidado da sauran mutane da suka ajiye aiki sunyi haka ne don basu iya yin aiki da canjin da ya zo dashi ba.

Gwamnan Bauchi ya bayyana dalilin da yasa mataimakinsa ya ajiye aiki

Gwamnan Bauchi ya bayyana dalilin da yasa mataimakinsa ya ajiye aiki

Gidado a takardar da ya rubuta ta ajiye aiki ya bayyana cewa cigaba da aiki ba alkhairi bane da adalci a tsakaninsa da gwamnan.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar matasan arewa ta goyi bayan sake zabar shugaba Buhari a matsayin shugaban kasa

Gwamnan ya bayyana cewa yazo da guguwar canji a jihar wadda zata canza irin rayuwar da mutane keyi ta fannin tafiyar da harkoki da ayyuka a jihar, wanda wannan canji kuma yake yiwa wasu wahalar karba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel