Zamu bayyana yadda PDP ta sace kudaden Najeriya ta jefa talakawa cikin talauci - Oshiomhole

Zamu bayyana yadda PDP ta sace kudaden Najeriya ta jefa talakawa cikin talauci - Oshiomhole

- Tsohon gwamnan jihar Edo Comrade Adams Oshiomhole, yace kamfen na 2019 a jam’iyyar APC zai yi dadi saboda jam’iyyar zata fallasa yadda gwamnatin datayi shekaru 16 akan mulki ta PDP ta sace kudaden al’umma ta jefa mutanen Najeriya cikin talauci

- Oshiomhole ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da shuwagabannin jam’iyyar ta APC a jihar Edo, duk da kokarin da jam’iyyar adawar keyi na ganin sun batawa APC suna a wurin ‘yan Najeriya ta hanyar yi musu karya akan abubuwan da gwamnatin ke aikatawa

- Oshiomhole ya bayyana cewa shugaba Buhari zai sake komawa kan kujerarsa ta shugaban kasa sakamakon ayyukan cigaba da ya kawo a kasar

Tsohon gwamnan jihar Edo Comrade Adams Oshiomhole, yace kamfen na 2019 a jam’iyyar APC zai yi dadi saboda jam’iyyar zata fallasa yadda gwamnatin datayi shekaru 16 akan mulki ta PDP ta sace kudaden al’umma ta jefa mutanen Najeriya cikin talauci.

Oshiomhole ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da shuwagabannin jam’iyyar ta APC a jihar Edo, duk da kokarin da jam’iyyar adawar keyi na ganin sun batawa APC suna a wurin ‘yan Najeriya ta hanyar yi musu karya akan abubuwan da gwamnatin ke aikatawa.

Zamu bayyana yadda PDP ta sace kudaden Najeriya ta jefa talakawa cikin talauci - Oshiomhole

Zamu bayyana yadda PDP ta sace kudaden Najeriya ta jefa talakawa cikin talauci - Oshiomhole

Oshiomhole ya bayyana cewa shugaba Buhari zai sake komawa kan kujerarsa ta shugaban kasa sakamakon ayyukan cigaba da ya kawo a kasar, kuma jam’iyyar ta APC zata kara lashe zaben gwamnoni a jihohin Najeriya da kuma kujerun ‘yan majalisu.

KU KARANTA KUMA: Hukumar EFCC ta tsare tsohon gwamnan jihar Kaduna Ramalan Yero har na tsawon sa’o’i 4 akan N700m na kudin kamfen

Oshiomhole ya kasance ya samu goyon bayan shugaba Muhammadu Buhari, cikin ‘yan kwanakin da suka gabata akan maye gurbin ciyaman na jam’iyyar tasu ta APC John Odigie-Oyegun.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel