Hukumar EFCC ta tsare tsohon gwamnan jihar Kaduna Ramalan Yero har na tsawon sa’o’i 4 akan N700m na kudin kamfen

Hukumar EFCC ta tsare tsohon gwamnan jihar Kaduna Ramalan Yero har na tsawon sa’o’i 4 akan N700m na kudin kamfen

- Hukumar yaki da rashawa a ranar juma’a ta tsare tsohon gwamnan jihar Kaduna Ramalan yero, har na tsawon awowi 4 a ofishinsu na jihar Kaduna

- Yero ya kasance a ofishin EFCC dake jihar Kaduna daga misalin karfe 9 na safe zuwa karfe 1:30 na rana, lokacin da ya fito daga ofishin da murmushi a fuskarsa

- Tsohon gwamnan yayi godiya ga magoya bayansa wadanda suka kasance a gaban ofishin don nuna kauna a gareshi har sai da yace su tafi masallaci saboda sallar juma’a

A ranar 25 ga watan Mayu, hukumar yaki da rashawa a ranar juma’a ta tsare tsohon gwamnan jihar Kaduna Ramalan yero, har na tsawon awowi 4 a ofishinsu na jihar Kaduna.

Yero ya kasance a ofishin EFCC dake jihar Kaduna daga misalin karfe 9 na safe zuwa karfe 1:30 na rana, lokacin da ya fito daga ofishin da murmushi a fuskarsa kamar yadda NAN ta ruwaito.

Tsohon gwamnan yayi godiya ga magoya bayansa wadanda suka kasance a gaban ofishin don nuna kauna a gareshi har sai da yace su tafi masallaci saboda sallar juma’a.

Hukumar EFCC ta tsare tsohon gwamnan jihar Kaduna Ramalan Yero har na tsawon sa’o’i 4 akan N700m na kudin kamfen

Hukumar EFCC ta tsare tsohon gwamnan jihar Kaduna Ramalan Yero har na tsawon sa’o’i 4 akan N700m na kudin kamfen

Duk da cewa Yero bai amince da yayi wani jawabi ga manema labarai ba, bayan fitowarsa daga ofishin na hukumar yaki da rashawa.

KU KARANTA KUMA: Wani yaro na kwance a asibiti bayan malaminsu na makaranta ya yi masa rauni a al’aurarsa

Mai magana da yawun tsohon gwamnan Malam Yakubu Lere, bayan haka ya bayyanawa NAN cewa an kira ubangidan nasa ne akan wasu kudade N700m na kudin kamfen wanda aka bawa jihar daga helikwatar jam’iyyar PDP a shekarar 2015.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel