Yanzu Yanzu: Babban jigon PDP kuma dan takarar gwamna Isiaka ya bar jam’iyyar gabannin zaben 2019

Yanzu Yanzu: Babban jigon PDP kuma dan takarar gwamna Isiaka ya bar jam’iyyar gabannin zaben 2019

- Prince Gboyega Isiaka, ya bayyana barinsa jam’iyyar ta PDP a wata takarda da ya rubutawa sakatariyar jam’iyyar dake jihar Ogun

- Isiaka yayi korafin cewa duk kokarin da aka yi na magance matsalolin dake damun jam’iyyar a Ogun abun ya gagara

- Isiaka ya bayyan cewa ya bar jam’iyyar ne da zummar komawa wata sabuwar jam’iyya gabanin zuwan zaben 2019

Dan takarar gwamna a jami’yyar PDP ta jihar Ogun a shekarar 2015 Prince Gboyega Isiaka, ya bayyana cewa ya bar jam’iyyar PDP duk da cewa abun ba sauki bane a gare shi.

Isiaka ya bayyana cewa ya yanke shawarar barin jam’iyyar ta PDP ne sakamakon an kasa magance matsalar dake bibiyar jam’iyyar a jihar Ogun gashi kuma wani babban zabe na sake karatowa.

Jaridar The New Telegraph ta ruwaito cewa ya rubuta takardar barin jam’iyyar ne a ranar 24 ga watan Mayu, ya kuma rubuta ta ne zuwa ga ciyaman na jam’iyyar na jihar.

Yanzu Yanzu: Babban jigon PDP kuma dan takarar gwamna Isiaka ya bar jam’iyyar gabannin zaben 2019

Yanzu Yanzu: Babban jigon PDP kuma dan takarar gwamna Isiaka ya bar jam’iyyar gabannin zaben 2019

Isiaka wanda ya kasance dan takarar jam’iyyar har sau biyu, yace tinda har sun kasa magance matsalar dake damun jam’iyyar shi zai barta ya koma wata sabuwar jam’iyyar adawa.

KU KARANTA KUMA: Abun na yi ne: An sake sace sandar kungiyar majalisar tarayya

Jam’iyyar ta PDP a jihar ta Ogun ta rabu biyu ne tsakanin Sanata Buruji Kashamu da Hon. Oladipupo Adebutu.

Wale Junaidu, daya daga cikin jam’ian Isiaka yace ubangidan nasa zai tsaya takara gwamna a 2019, amma dai bai bayyana ko a wace jam’iyya zai tsaya takarar ba, sannan ya bayyana cewa Isiaka zai gudanar da gwamnatinsa bisa tsarin jama’a idan har aka zabe shi a 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel