Wani yaro na kwance a asibiti bayan malaminsu na makaranta ya yi masa rauni a al’aurarsa

Wani yaro na kwance a asibiti bayan malaminsu na makaranta ya yi masa rauni a al’aurarsa

- An kwantar da wani yaro dan makarantar Firamare a asibiti a ranar Alhamis bayan malaman makarantarsu uku sun hadu sun masa duka inda har suka yi masa rauni a marainansa

- Lamarin ya faru ne a makarantar Firamare na Kamukunji a kasar Kenya, inda likitoci ke shirya shigar da yaron dakin fida domin yi masa aiki a marainan nasa

- Mary Wangeci, mahaifiyar yaron ta amsa kiran wayar salula daga shugaban makarantar, inda ya sanar da ita lamarin da ya auku

An kwantar da wani yaro dan makarantar Firamare a asibiti a ranar Alhamis bayan malaman makarantarsu uku sun hadu sun masa duka inda har suka yi masa rauni a marainansa.

Lamarin ya faru ne a makarantar Firamare na Kamukunji a kasar Kenya, inda likitoci ke shirya shigar da yaron dakin fida domin yi masa aiki a marainan nasa da malaman suka raunata wurin dukan yaron.

Mary Wangeci, mahaifiyar yaron ta amsa kiran wayar salula daga shugaban makarantar, inda ya sanar da ita lamarin da ya auku da yaronta.

Wani yaro na kwance a asibiti bayan malaminsu na makaranta ya yi masa rauni a al’aurarsa

Wani yaro na kwance a asibiti bayan malaminsu na makaranta ya yi masa rauni a al’aurarsa

Bayan nan ta samu labari daga abokanan dan nata cewa malamai ne suka masa duka har aka kai shi karamin asibi na Ngano domin samun taimakon gaggawa kafin aka mayar dashi zuwa babban asibitin Nyahururu.

KU KARANTA KUMA: Dandalin kannywood: Rahma Sadau ta samu lambar yabo a matsayin jarumar jarumai na shekara

Daga jin haka mahaifiyar yaron ta kai kara a ofishin ‘yan sanda na Ngano, amma dai ba’a kai ga kama ko daya cikin malaman ba sakamakon guduwa da suka yi bayan samun labarin cewa an kira ‘yan sanda.

Hakan ya jawo mazauna yankin gudanar da zanga-zanga a ranar Juma’a, inda suka bukaci sai an kamo malaman uku an hukuntasu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel