A wata mai zuwa ne kasargumin mai garkuwa da mutane Evans zai san makomansa

A wata mai zuwa ne kasargumin mai garkuwa da mutane Evans zai san makomansa

Wata babban kotu a jihar Legas ta saka ranar 26 ga watan Yuni don yanke hukunci a kan bukatar da attajirin mai garkuwa da mutane Chukwudumeme Onwuamadike wanda aka fi sani da Evans ya shigar na yin watsi da tuhumar laifukan da ake masa.

Alkalin kotun, A. Akintoye ya tsayar da ranar ne bayan ya yi watsi da wata karar da Evans ya shigar inda ya yi ikirarin cewa tuhume-tuhumen da ake masa sun sabawa ka'idojin shari'ar a kotu.

KU KARANTA: An damke sojoji da tsaffin 'yan sandan cikin gungun wasu 'yan fashi da makami

A cewar lauyan Evans, Olukoya Ogungbeje, ya ce an gwamnatin jihar Legas ta shigar da wasu kararaki masu kamamceceniya da wannan a wasu kotuna biyu da ke jihar. Ya ce tuhume-tuhume na tattare da kurakurai da maimaici kuma hakan bata lokacin kotu ne.

Gobe kasurgumin mai garkuwa da mutane Evans zai san makomansa

Gobe kasurgumin mai garkuwa da mutane Evans zai san makomansa

Ogunbeje ya yi nuni ga sashi na 153 na dokar tabbatar da laifi na jihar Legas inda ya ce babu wani doka da ta hana masu tuhumar su shigar da kararakin wajen Alkali guda tunda wasu tuhume-tuhumen duk na laifi iri daya ne.

Da hakan ne Ogungbeje ya roki kotun tayi watsi da tuhume-tuhumen da ake wa wanda ya ke karewa.

A yayin da take mayar da martani, lauya mai shigar da kara, Titilayo Shitta-Bey ya ce abinda doka ya tanada shine kowace laifi a ware ta daban. "Saba doka ne tattara laifuka guda biyu cikin kara guda," inji ta.

Ta kara da cewa ana tuhumar Evans da yunkurin kashe wani mai suna James Uduji ne a karar ta uku, sannan kuma a kara ta hudu ana tuhumarsa da yunkurin kashe wani Donald Nwoye ne.

Ta kuma ce sauran kararakin da aka shigar a kan Evans a wasu kotunan sun shafi wasu mutanen daban ne saboda hakan ta bukaci kotu tayi fatali da bukatar da Evans ya shigar.

Bayan sauraron lauyoyin, alkalin kotun ta dage yanke hukunci a shari'ar zuwa ranar 26 ga watan Yuni.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel