Gwamnatin Jihar Ekiti tayi wa tsohon shugaba Jonathan wata babban karamci

Gwamnatin Jihar Ekiti tayi wa tsohon shugaba Jonathan wata babban karamci

- Gwamnatin jihar Ekiti ta raya sunan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan

- Gwamnatin ta sanya sunansa a gidan saukan shugaban kasa da ke gidan gwamnati a Ado Ekiti

- Sanarwan ta fito ne daga bakin mai magana da yawun gwamnatin jihar Ekiti, Lere Olayinka

Gwamnatin jihar Ekiti tayi wa tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan wata babban karamci inda ta saka sunansa a sabuwar gidan gwamnati na saukan shugaban kasa da aka kaddamar a yau Juma'a.

Mai magana da yawun gwamnatin jihar Ekiti, Lere Olayinka ne ya bayar da sanarwan ta shafinsa na dandalin sada zumuntar Facebook na sanya sunan na 'Ebele Goodluck Jonathan Presidential Lodge'.

Jihar Ekiti tayi wa tsohon shugaba Jonathan wata babban karamci

Jihar Ekiti tayi wa tsohon shugaba Jonathan wata babban karamci

KU KARANTA: Rikcin jihar Ribas: Shugaba Buhari ya sake ganawa da gwamna Okorocha

Jihar Ekiti tayi wa tsohon shugaba Jonathan wata babban karamci

Jihar Ekiti tayi wa tsohon shugaba Jonathan wata babban karamci

Kalamansa: "A yau a garin Ekiti, za'a rada wa gidan gwamnati na saukan shugaban kasa da ke Ado Ekiti sunan tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan."

Wannan karamawar tana zuwa ne a lokacin da gwamnati mai ci yanzu ta ke kokarin bibiyar mukaraban tsohon shugaban kasa wanda ake tuhuma da wadaka da dukiyoyin al'umma a yayinda suke gwamnati.

Mutane masu amfani da dandalin sada zumuntar na Facebook sun tofa albarkacin bakinsu a kan karamawar da akayi wa tsohon shugaban kasa, wasu na ganin ya cancanci irin wannan karamawar inda wasu kuma ke ganin bai tsinana wani abin alkhairin da har za'ayi masa wannan karamawar ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel