Yansanda sun kwato sandar ikon majalisar Dokokin jihar Gombe da yan majalisar suka sace

Yansanda sun kwato sandar ikon majalisar Dokokin jihar Gombe da yan majalisar suka sace

Rundunar Yansandan jihar Gombe ta bayyana cewar ta gano sandan ikon majalisar dokokin jihar Gombe da aka sace a ranar Alhamis 24 ga watan Mayu, kamar yadda kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito.

Kwamishinan Yansandan jihar Shina Olukolu ne ya sanar da haka a ranar Juma’a 25 ga watan Mayu, inda yace sun gano sandar ne da safiyar ranar Juma’a a bayan Kotun ma’aikata dake garin Gombe.

KU KARANTA: Bahallatsar Shekarau da EFCC: Rashin adalcin Buhari ne – Inji magoya baya

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wasu yan majalisar ne su hudu suka sace sandan a ranar ALhamis da misalin karfe 1:30 na rana, biyo bayan gazawar kokarin da suka yi na ganin sun tsige shuwagabannin marasa rinjaye na majalisar gaba daya.

Yansanda sun kwato sandar ikon majalisar Dokokin jihar Gombe da yan majalisar suka sace

Sandar

“Bayan samun labarin abinda ya faru sai Kwamishinan Yansandan ya kai ziyara majalisar, inda ya kara karfafa tsaro a majalisar, saa’annan ya dauki alwashin binciko sandar kamar yadda babban sufetan Yansandan suka kawo.” Inji shi.

Dayake karbar sandar, Kaakakin majalisar dokokin jihar Gombe, Alhaji Nasiru Nona yay aba da kokarin da jami’an Yansanda da sauran hukumomin tsaro da suka tashi tsaye wajen ganin sun kwato kwato sandar nan.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel