Wani jigo a APC ya huro wa Dogara wuta, ya bukaci a kore shi daga jam'iyya

Wani jigo a APC ya huro wa Dogara wuta, ya bukaci a kore shi daga jam'iyya

- Wani jigo a jami'iyyar APC reshen jihar Bauchi ya bukaci a kore kakakin majalisar Dogara daga jam'iyyar

- Ya ce Dogara da mukarrabansa ne suka kai jam'iyyar kara kotu ba tare da bin ka'idojin sulhu da jam'iyya ta shimfida ba

- Dogara da wasu yan jam'iyyar sun kai kara kotu ne inda suke bukatar a soke zabukkan da akayi a taron jam'iyyar

Wani jigo a jam'iyyar APC daga jihar Bauchi, Ali Saidu, ya huro wa kakakin majalisar wakilai, Honarabul Yakubu Dogara wuta inda ya ke bukatar a sallame shi daga jam'iyya.

Saidu ya furta hakan ne a hedkwatan yan a ware na jam'iyyar APC a a Bauchi inda ya ce magoya bayan kakakin majalisar a jam'iyyar ne sukayi sanadiyyar maka jam'iyyar a kotu kamar yadda Nigeria News ta ruwaito.

Wani jigo a APC ya huro wa Dogara wuta, ya na son kore shi daga jam'iyya

Wani jigo a APC ya huro wa Dogara wuta, ya na son kore shi daga jam'iyya

KU KARANTA: Abinda yasa muka matsar da taron gangamin kasa zuwa 23 ga watan Yuni - APC

A cewarsa, "Ana tsamanin idan wasu yan jam'iyya suna ganin an yi musu ba dai-dai ba sa fara gabatar da kokensu ga hedkwatan jam'iyya na kasa kuma su saurari sakamakon hukunci kafin su tafi kotu tunda haka dokan jam'iyya ya tsara amma sai suka tafi kotu ba tare da jiran sakamako daga hedkwatar kasa ba."

Idan ba'a manta ba, Kakakin majalisar, Dogara da tsohon ministan harkokin yan sanda, Dr. Yakubu Ibrahim Lame da tsohon dan majalisa daga Toro, Barrister Zailaini da dan majalisar jihar Bauchi Hon. Aminu Tukur da wasu sun kai APC kara a wata babban kotun Abuja inda suke bukatar n soke zabukkan da akayi a taron jihar wai saboda anyi magudi.

Saidu ya yi ikirarin cewa irin wannan halayyar da Dogara ke nunawa ya tabbatar da jita-jitar da ke yaduwa a gari na cewa suna gab da canja sheka zuwa jam'iyyar adawa.

Ya kuma cigaba da cewa "Mafi yawanci wadanda ke kai jam'iyya kara kotu suna hakan ne saboda fargaban rasa kujerunsu idan zaben 2019 ta zo, hakan yasa suke neman inda za su fake saboda sun san al'umma basu tare da su."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel