Uwar gidan Fani-Kayode ta haifi 'yan 3 reras

Uwar gidan Fani-Kayode ta haifi 'yan 3 reras

Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu rahoton cewa, Precious Chikwendu, uwargidan tsohon Ministan jiragen Sama, Femi Fani-Kayode, ta haifi jariran ta 'yan uku reras a ranar yau ta Juma'a.

Tsohon ministan ne ya bayyana hakan a shafin sa na dandalin sada zumunta ta twitter.

Jariran 'yan uku wanda dukkanin su maza ne mahaifin na su ya bayar da sunayen su kamar haka; Ragnar, Aiden da kuma Liam.

Uwar gidan Fani-Kayode ta haifi 'yan 3 reras

Uwar gidan Fani-Kayode ta haifi 'yan 3 reras

Legit.ng ta fahimci cewa, a yau wannan rana 25 ga watan Mayu ta yi daidai da ranar haihuwar uwargidan tsohon Ministan da wasu ke cewa ta samu baiwa.

KARANTA KUMA: Goron Azumi: Ku tsaya ku rika hutawa a yayin da gajiya ta cimmaku a wannan lokuta na Azumi - Hukumar FRSC ga Direbobi

Ma'abota dandalin sada zumunta sun taya murna ga tsohon Ministan dangane da wannan babban rabo da ya samu, inda suka rinka aiko sakonni na son barka daban-daban.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel