Yanzu-yanzu: Kujerar Osinbajo na rawa - Buhari

Yanzu-yanzu: Kujerar Osinbajo na rawa - Buhari

Yayinda zaben 2019 ya gabato, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa kujerar mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, na fuskantar barazana.

Shugaban kasan ya bayyana hakan ne a yau Juma'a, 25 ga watan Mayu a fadar shugaban kasa yayinda wata tawagar gamayyar mata yan majalisa a Najerya suka kawo masa ziyara.

Shugaba Buhari ya bayyana niyyar tazarce amma bai bada tabbacin cewa zai cigaba da mataimakinsa ba.

Yanzu-yanzu: Kujerar Osinbajo na rawa - Buhari

Yanzu-yanzu: Kujerar Osinbajo na rawa - Buhari

Yayinda yake amsa tambayar yan kungiyar kan bukatar mace mataimakin shugaban kasa, Buhari ya fada cikin wasa cewa: "Allah sarki mataimakin shugaban kasa baya nan, amma sakataren gwamnati zai fada masa cewa kujerarshi na fuskantar barazana."

"Mataimakin shugaban kasa kadai zai shafa. idan muka ci zaben mai zuwa, da yiwuwan ya rasa nasa."

Buhari ya jawo hankalin matan da su daina yarda da maganan cewa mazaje azzalumai ne kuma basu son alaka da mata a siyasa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel