Taron Jam'iyyar APC: Shugaba Buhari ya yi wata ganawa da Adams Oshiomhole

Taron Jam'iyyar APC: Shugaba Buhari ya yi wata ganawa da Adams Oshiomhole

A ranar Alhamis din da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomhole.

Kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ya ruwaito, ganawar ta sirrance ta wakana ne a ofishin shugaba Buhari dake fadar sa ta Villa inda suka kwashi kimanin sa'o'i biyu a bayan labule.

Jaridar ta ruwaito cewa, wannan ganawa ta kuma hadar da shugaban kungiyar gwamnonin jam'iyyar APC, Gwamna Rochas Okorocha na jihar Imo da yayi rakiyar Oshiomhole zuwa fadar ta shugaban kasa.

Hasashen maname labarai ya bayyana cewa, ta yiwu wannan ganawar ta gudana a sakamakon taron jam'iyyar da aka shirya gudanar a watan Yuni mai gabatowa.

Taron Jam'iyyar APC: Shugaba Buhari ya yi wata ganawa da Adams Oshiomhole

Taron Jam'iyyar APC: Shugaba Buhari ya yi wata ganawa da Adams Oshiomhole

Legit.ng ta fahimci cewa, Oshiomhole shine dan takarar da ake hasashen zai maye gurbin kujerar shugaban jam'iyyar, Cif John Odigie Oyegun, a sakamakon goyon baya da ya samu na shugaba Buhari da kuma wasu gwamnonin jam'iyya.

KARANTA KUMA: Yadda kwatsam na sadu da diya ta - Mahaifiyar 'Dalibar Dapchi ta Karshe dake hannun 'Yan Boko Haram

A kwana-kwanan nan shugaba Buhari ya nemi gwamnonin jam'iyyar akan su goyi bayan Oshiomhole wajen cin gajiyar kujerar jam'iyyar ta su.

Ko shakka babu Oshiomhole ya samu goyon baya na kanwa uwar gamin matsalolin jam'iyyar, tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Ahmad Bola Tinubu.

Yayin da ganawar tsohon gwamnan da shugaba Buhari ta zo karshe, sun kama hanyar su tare da Okorocha ba tare da ko bi ta kan manema labarai na fadar shugaban kasa da suka nemi karin haske akan ganawar ta sirrance.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel