Rikcin jihar Ribas: Shugaba Buhari ya sake ganawa da gwamna Okorocha

Rikcin jihar Ribas: Shugaba Buhari ya sake ganawa da gwamna Okorocha

A jiya Alhamis, shugaba Muhammadu Buhari ya yi wata ganawar siri tare da gwamna Rochas na jihar Imo da tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomole a fadar Aso Villa da ke Abuja.

Wannan ganawar da Okorocha ya yi da shugaba Buhari na tsawon sa'a daya shine ganawa ta biyu bayan sun gana da shugaban kasar kwanakin baya a lokacin daya kai masa ziyara a Daura.

Gwamnan ya bayyana rashin gamsuwarsa a kan yadda aka gudanar da zabukkan kananan hukumomi a jam'iyyar ta APC ta yi a jihar Imo. Sai dai Okorocha bai zanta da manema labarai ba bayan taron.

Rikcin jihar Ribas: Shugaba Buhari ya sake ganawa da gwamna Okorocha

Rikcin jihar Ribas: Shugaba Buhari ya sake ganawa da gwamna Okorocha

KU KARANTA: An damke sojoji da tsaffin 'yan sandan cikin gungun wasu 'yan fashi da makami

Idan ba'a manta ba a ranar 7 ga watan Mayu wannan shekarar, Okorocha ya shaidawa manema labarai a garin Daura cewa ba'a gudanar da zabukan kananan hukumomi a jihar Imo ba bayan ganawarsa da shugaba Buhari.

Kalamansa: "Muna tsamanin a gudanar da siyasar cikin gida yadda ta dace saboda hakkan ne yafi alkhairi. Dole a dena siyasa mara tsafta inda zaka ga ana sace akwatunan zabe da takardun sakamakon zaben.

"Na shaidawa shugaban kasa abubuwan da ke faruwa kuma zamu tabbatar da cewa hakan bai sake faruwa ba."

Okorocha da magoya bayansa sun kauracewa taron kananan hukumomi na jam'iyyar APC da akayi a jihar inda suka bukaci a sake tsayar da rannan da za'a gudanar da taron gudumomi.

A yayin da Okorocha ke jawabi ga magoya bayansa a jihar, ya shaida musu cewa ba za gudanar da taron kananan hukumomi a jihar ba har sai an warware matsalar da ake fama da ita a gundumomin jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel