Ragowar yarinyar Dapchi da ke hannun Boko Haram ba ta dawo gida ba har yanzu

Ragowar yarinyar Dapchi da ke hannun Boko Haram ba ta dawo gida ba har yanzu

- Kwanaki aka maido Yaran nan na Makarantar Dapchi da aka sace

- Sai dai har yanzu guda 1 tana hannun ‘Yan ta’addan na Boko Haram

- An yi alkawarin ceto Leah Sharibu amma har yanzu babu labarin ta

Kwanaki dai ‘Yan ta’addan Boko Haram su ka sace wasu ‘Yan Makarantar Gwamnati ta ‘Yan Mata da ke Garin Dapchi a Jihar Yobe. An yi nasarar maido yaran illa guda 1 mai shekaru 15 a Duniya da aka cigaba da tsare ta saboda addinin ta.

Ragowar yarinyar Dapchi da ke hannun Boko Haram ba ta dawo gida ba har yanzu

Gwamnati tace tana bakin kokari na sakin Leah Sharibu
Source: Depositphotos

A baya mun ji cewa ‘Yan ta’addan za su saki yarinyar da su ka rike mai suna Leah Sharibu. Sufetan ‘Yam Sanda na Kasar Ibrahim K. Idris ne ya bayyana wannan a watan Jiya lokacin da yake magana da ‘Yan Jarida a Garin Maiduguri.

‘Yan Boko Haram din sun ki sakin yarinyar ne saboda ta ki karbar musulunci ta rike addinin ta na Kiristanci. Wannan dai ya sa manyan Kungiyoyin Kiristoci su kace sama da kasa za ta hade idan har ba a ceto wannan yarinya ba.

KU KARANTA: An shiga gidan wani yaron tsohon Shugaban kasa Jonathan

Ibrahim Idris wanda shi ne IG na ‘Yan Sanda yayi alkawarin cewa ba da jimawa ba za a saki wannan yarinya lokacin da ya kai ziyara Jihar Borno. Fiye da wata daya kenan dai da yin wannan maganar amma har yanzu shiru.

Daga baya dai ‘Yan Sanda sun karyata cewa sun yi alkawarin ceto wannan yarinya. Yarinyar da ke Makarantar ta Dapchi ta cika shekara 15 ne a Duniya kwanaki a hannun ‘Yan ta’addan inda har yanzu ‘Yan uwan ta ke cikin jimami.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel