Dalilin da yasa Obasanjo ke fushi da Shugaba Buhari - Fadar Shugaban Kasa

Dalilin da yasa Obasanjo ke fushi da Shugaba Buhari - Fadar Shugaban Kasa

A ranar Alhamis din da ta gabata ne fadar shugaban kasa ta bayyana cewa, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo yana kullace da shugaban kasa Muhammadu Buhari ne a sanadiyar inganta wutar lantarki ta kasar nan da ya yi.

Babbar hadima ta musamman ga shugaban kasa akan sabuwar hanyar sadarwa ta dandalan sada zumunta, Lauretta Onochie, ita ta bayyana hakan yayin da take kushe gwamnatin tsohon shugaban kasar dangane da wutar lantarki.

Misis Lauretta ta bayyana cewa, ko shakka babu gwamnatin shugaba Buhari ta ci gajiyar kasar nan cikin duhu na rashin wutar lantarki.

Lauretta Onochie

Lauretta Onochie

Ta ci gaba da cewa, wannan lamari ya fayyace tsakanin zare da abawa dangane da banbanci tsakanin shugaba Buhari da kungiyar tsaffin shugabanni da suka haɗa gwiwa da tsohon shugaba Obasanjo masu akida ta cin hanci da rashawa.

KARANTA KUMA: Mun kayyade ranar mika Kasafin Kudin 2018 zuwa ga Shugaba Buhari - Saraki

Legit.ng ta fahimci cewa, a ranar Talatar da ta gabata ne shugaba Buhari ya jirwaye mai kama da wanka dangane da yadda wani tsohon shugaban kasa ya batar da dalar Amurka Biliyan 16 a sashen wutar lantarki wanda kawowa yanzu ba bu amo ballanta labari na tasirin haka.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan yayin da tawagar magoya bayan sa ta ziyarce a fadar sa wadda shugaban hukumar kastam, Kanal Hameed Ali ya jagoranta, inda ya kada baki da cewar "ko ina wutar lantarkin take?"

Rahotanni sun bayyana cewa, Obasanjo yayi martanin kan wannan kalubale na shugaba Buhari da sanadin hadimin sa, Kehinde Akinyemi, inda yace a shirye yake akan a yi masa titsiye.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel