An damke sojoji da tsaffin 'yan sandan cikin gungun wasu 'yan fashi da makami

An damke sojoji da tsaffin 'yan sandan cikin gungun wasu 'yan fashi da makami

An kama wani jami'in sojan ruwa da wasu sojojin kasa da kuma tsaffin jami'an yan sanda cikin gungun wasu yan fashi da makami 50 da ake tuhuma da aikata laifukan da suka hada da garkuwa da mutane da fashi a jihar Oyo.

A lokacin da ya ke jawabi ga manema labarai a hedkwatan hukumar da ke Eleyele, Ibadan, Kwamishinan yan sanda, Mr. Abiodun Odude ya ce an kama sojin ruwan tare da yan kungiyarsa guda 12 wanda SARS sun dade suna neman su.

Ya ce: "An kama shida daga cikinsu ne a mafakarsu da ke Ilasa a garin Ogbomoso, daga nan kuma suka taimaka aka kama sauran yan kungiyar guda hudu a wurare daban-daban."

Ana zaton wuta a makera: An damke sojoji da tsaffin 'yan sandan cikin gungun wasu 'yan fashi da makami

Ana zaton wuta a makera: An damke sojoji da tsaffin 'yan sandan cikin gungun wasu 'yan fashi da makami

Odude ya yi karin bayani inda ya ce sojin da sauran yan kungiyar sukan sanya khakin soji ne lokacin da zasu tafi zuwa aikata fashin su.

KU KARANTA: Jonah Jang yana alfahari da zuwa gidan yari, ya ce ya kafa wata tarihi

Daya daga cikin sojojin da aka kama, Private Azeez Olaide mai shekaru 22 da ya yi aiki a bataliya na 202 Bama Maiduguri ya ce sukan tsare motocci a kan titi ne idan suka ga maukin motan ya yi kama da dan damfarar yanar gizo wato Yahoo Boy.

Idan mutum ya gaza nuna katin shaida sai su nemi ya basu cin hanci har ma wasu lokutan suna barzanar kashe mutum idan bai basu abinda suke so ba.

"Wanda muka kama daga karshe yana tare da budurwarsa ne kuma sun kai su KS Motel Otel da ke Mobil road inda muka yiwa budurwar fyade kuma muka karbi N145,000 daga hannun ta." inji Azeez.

Shi kuma tsohon dan sandan mai suna Femi John ya ce an kore shi daga aikin dan sanda ne bayan an kama shi ya karkatar da lita 33,000 na man fetur da aka umurci shi ya raka daga Apata zuwa Fiditi kusa da jihar Oyo.

"Hakan yasa aka sallame ni daga aiki a 2012 amma na cigaba da sanya kayan aiki na ina karabar kudade hannun mutane saboda ina bukatar kudi don ciyar da iyali na." inji shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel