Ba da dukkan mu Shugaba Buhari yake magana ba, wasu tsirarru ya soka - Majalisa

Ba da dukkan mu Shugaba Buhari yake magana ba, wasu tsirarru ya soka - Majalisa

Majalisar Wakilan Tarayya ta maidawa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari martani ta bakin Honarabul Abdulaziz Namdas game da wasu kalaman sa da yayi kwanan nan a Fadar Shugaban kasa lokacin da ya gana da 'Yan BSO..

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi kaca-kaca da wasu ‘Yan Majalisar Kasar inda yace wasu sun fi shekara 10 amma babu aikin da su ke tsinanawa Najeriya. Da alamu wannan maganar ko kadan bai sosawa 'Yan Majalisar rai.

Ba da dukkan mu Shugaba Buhari yake magana ba, wasu tsirarru ya soka - Majalisa

Majalisa tace akwai matsala idan Buhari ya soki dukkan su

Shugaban Kwamitin harkokin yada labarai watau Honarabul Abdulaziz Namdas ya maidawa Shugaban Kasar amsa a farkon makon nan inda yace Shugaban Kasar na da damar ya bayyana ra’ayin sa game da 'Yan Majalisar Tarayyar.

Abdulrazak Namdas ya bayyana wannan ne lokacin da yake magana da manema labarai a Birnin Tarayya Abuja. Hon. Namdas yace Shugaban Kasar na da damar bayyana ra’ayin sa a kan aikin da ‘Yan Majalisar kasar ke yi.

KU KARANTA: Kudirin Shugaban Kasa ya raba kan Sanatocin Arewa da na Kudu

Shugaban kasar dai ya kalubalanci ‘Yan Majalisar su yi gaba-da-gaba da shi inda yace babu Gwamnatin da ta ware tsabar kudi domin yi wa kasa aiki irin sa. Majalisar ita ma da kan ta dai ta yabawa kokarin Shugaban Kasa Buhari kan wannan.

Majalisa tace duk ‘Dan Majalisar da ba ya aikin da aka turo shi zai gamu da fushin mutanen da su ka zabe sa don haka ne ma wasu ke faduwa zabe na gaba. Namdas yace da wasu ‘Yan Majalisa tsirarru Buhari ke magana ba dukkan su ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel